Siyasar Adamawa: Babachir da Ribadu sun hade kai domin yakar sakataren gwamnatin Buhari

Siyasar Adamawa: Babachir da Ribadu sun hade kai domin yakar sakataren gwamnatin Buhari

- Wasu manyan ‘ya’yan APC a Adamawa sun yi watsi da shawarar da jam’iyyar ta dauka a jihar na fitar da ‘yan takarar ta hanyar amfani da wakilai (daliget)

- A sahun gaba cikin masu adawa da tsarin amfani da daliget wajen fitar da ‘yan takara a jihar Adamawa akwai Babachir David Lawal da Malam Nuhu Ribadu

- A bangaren masu son a yi amfani da daliget akwai Boss Gida Mustapha, sakataren gwamnatin shugaba Buhari da kuma gwamnan jihar, Umar Jibrilla

Babachir David Lawal, tsohohon sakataren gwamnatin shugaba Buhari, da Malam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) tare da wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a jihar Adamawa sun yi watsi da batun zaben fitar da ‘yan takarar ta hanyar amfani da wakilai(daliget).

A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar Adamawa karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha, suka yi taro tare da amincewa da fitar da ‘yan takara ta hanyar amfani da daliget.

Siyasar Adamawa: Babachir da Ribadu sun hade kai domin yakar sakataren gwamnatin Buhari
Babachir David Lawal
Asali: Depositphotos

Sai dai da yake Magana da manema labarai a yau, Lahadi, Babachir ya ce basu da masaniyar wancan taron da aka yi domin a sirrance aka yi shi.

Babachir ya bayyana cewar fitar da ‘yan takara ta hanyar amfani da daliget zai shafi nasarar jam’iyyar APC a jihar Adamawa a zabukan shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Ministocin Buhari da suka yi murabus don kashin kan su

Babachir na wannan kalamai ne da yawun ragowar masu ruwa da tsaki da basu amince da matakin das u Boss Mustapha suka dauka ba.

Bayan Babachir da Ribadu, ragowar masu ruwa da tsaki a APC a jihar dake tare da su a kan wannan mataki akwai; Ahmed Abubakar Mo’Allayidi, Abubakar Halilu Girei, Bello Tukur, Marcus Gundiri, Sadiq Muhammed da Mahmoud Halilu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel