Tonon silili: Wani dan luwadi ya zayyana wadanda suka taba kwana da shi a Najeriya

Tonon silili: Wani dan luwadi ya zayyana wadanda suka taba kwana da shi a Najeriya

- Wani dan luwadi ya zayyana wadanda suka taba kwana da shi a Najeriya

- Yace akwai manyan malamai da kuma 'yan siyasa

- Yace kuma a fili nunawa sukeyi kamar suna kyamar luwadin

Wani tattacen marar kunya kuma fitsararre da ya bayyana kan sa a matsayin dan luwadi a Najeriya mai suna Kahinde Bademosi ya lissafa wasu daga cikin wadanda yayi ikirarin suna kwanciya da shi daga cikin manya a Najeriya.

Tonon silili: Wani dan luwadi ya zayyana wadanda suka taba kwana da shi a Najeriya
Tonon silili: Wani dan luwadi ya zayyana wadanda suka taba kwana da shi a Najeriya
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kannywood: Auren wata jaruma ya mutu bayan kasa da watanni 3

Fitsararren, Kahinde Bademosi yace akwai munafunci sosai a game da maganar luwadi a Najeriya domin kuwa mafi yawacin masu yin luwadin a boye sune a kan gaba wajen sukar wadanda suka fito fili suka bayyanawa duniya kan su.

Legit.ng ta samu a cewar Kahinde, shi manyan Sanatoci da malaman addinai a Najeriya sun sha neman sa su kuma kwanta da shi amma kuma suna daga cikin sahun farko na masu sukar ta su a bainar jama'a.

Ya cigaba da cewa ko a 'yan kwanakin nan akwai Sanatan da ya kwanta da shi amma ba zai yi mamaki ba idan aka tada maganar auren jinsi a majalisar ya shiga cikin masu sukar.

A wani labarin kuma, Wasu matasa a jihar Osun dake a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya sun cafke wani fitaccen dan siyasa a jihar ta su dake zaman shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye yana wanka a tsirara cikin jeji.

Shi dai shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye, an ce wankan da aka kama shi yana yi baya rasa nasaba da tsafi irin na 'yan tsubbu da kan sa 'yan siyasa yi musamman ma ganin zabukan 2019 na kara karatowa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel