Jam’iyyar APC ta yi wa Gwamna Jibrilla mubaya’a a Jihar Adamawa

Jam’iyyar APC ta yi wa Gwamna Jibrilla mubaya’a a Jihar Adamawa

Shugabannin Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Adamawa sun zabi Jibrilla Bindow a matsayin ‘Dan takarar su na Gwamna a zaben 2019. Shugaban APC na Jihar ya bayyana wannan jiya wajen wani taron da aka yi a Hedikwatar APC a Garin Yola.

Jam’iyyar APC ta yi wa Gwamna Jibrilla mubaya’a a Jihar Adamawa
Gwamna Bindow da Shugaba Buhari a fadar Shugaban kasa
Asali: Depositphotos

Alhaji Ibrahim Bilal wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar APC a Adamawa ya bayyana cewa ‘Dan takarar Gwamna guda APC ta sani a 2019 kuma shi ne Mai Girma Umar Jibrilla Bindow. Bilal yace APC ta Adamawa tana tare da Gwamna.

Shugaban APC na Jihar ta Adamawa ya ja-kunnen masu harin kujerar Gwamnan inda ya fada masu cewa su san ba su da rabo tun yanzu. Bilal ya caccaki wadanda ya kira ‘Yan siyasar Abuja cewa su san Adamawa ta Gwamna Bindow ce.

KU KARANTA: An yi doke-doke wajen rikcin APC a Jihar Bauchi

Ibrahim Bilal da sauran Kusoshin APC a Adamawa sun nuna cewa Kanin Matar Shugaban Aisha Muhammadu Buhari wanda ya fito takarar Gwamna a APC ba zai kai labari ba. Alhaji Bilal yace APC tana tare da Shugaban kasa Buhari a sama.

Magoya-bayan Shugaba Buhari a Jihar Adamawa dai sun nuna cewa ba su tare da Shugaban APC a kan wannan batu. Wadanda ke tare da Shugaban kasar ba su halarci wannan taro ba inda aka tsaida Gwmana mai-ci a matsayin ‘Dan takarar APC.

Kwanaki kun ji cewa rikicin Jam’iyyar APC yayi kamari a Jihar Adamawa bayan da Magoya bayan Gwamnan Jihar su ka gargadi Shugaban APC Adams Oshimhole sabon tsarin zaben fitar da gwani da ya kawo na kato-bayan-kato a APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel