Me Ya Yi Zafi? APC Ta Sauya Ranar Zaɓen Fitar da Gwanin Shugaban Kasa, Gwamnoni
- Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sake sauya jadawalinta game da zaben fitar da gwani da ake shirin yi a Najeriya
- APC ta dage zaben fitar da gwani na shugaban kasa daga ranar da aka sanya daga farko kamar yadda tsara
- Mataimakin sakataren yada labarai, Duro Meseko, ya ce an yi sauye-sauye a jadawalin 2027, ciki har da duba takardu da sauraron korafe-korafe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar APC ta sauya zaben fitar da gwani na shugaban kasa wanda aka shirya yi a watan Mayun 2026.
Tun farko, jam'iyyar ta shirya gudanar da zaben fitar da gwanin shugaban kasa a tsakiyar watan Mayun 2026.

Source: Twitter
APC ta sauya ranar zaben fitar da gwani
Majiyoyi daga The Nation sun tabbatar da cewa an dage zaben daga ranar 15 da 16 ga Mayu zuwa ranar 23 ga Mayu 2026.
Haka kuma, zaben fitar da gwani na gwamna zai gudana a ranar 21 ga Mayu 2026, bisa sabon jadawalin da aka fitar domin shirye-shiryen zaben 2027.
Mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar, Duro Meseko, ne ya bayyana hakan bayan kammala taron kwamitin gudanarwa na kasa karo na 186 da aka gudanar a Abuja.
Ya ce an yi sauye-sauye a jadawalin, ciki har da jinkirta duba takardun ‘yan takara da kuma sauraron korafe-korafe.
Meseko ya bayyana cewa sayar da fom din takara zai fara daga 25 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu, 2026.
Ya kara da cewa ranar karshe ta mika fom din da aka cika ita ce 4 ga Mayu, sannan za a gudanar da tantance ‘yan takara daga 6 zuwa 9 ga Mayun 2026.

Source: Twitter
Yaushe za a yi zabukan fitar da gwani?
A cewarsa, za a sanar da sakamakon tantancewar a ranar 11 ga Mayu, yayin da kwamitocin daukaka kara za su fara aiki daga 12 zuwa 13 ga Mayu 2026.
Bayan haka, za a fara gudanar da zabukan fitar da gwani daga 15 zuwa 23 ga Mayun 2026, bisa jadawalin da aka tsara.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa za ta yi amfani da hanyoyin zabe guda biyu kamar yadda dokar zabe ta 2026 ta tanada, wato zaben kai tsaye da kuma sulhu.
An kuma jaddada cewa duk mai sha’awar takara yana da ‘yancin sayen fom, ba tare da wani takura ba kamar yadda Vanguard ta ce.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanya ranar 16 ga Janairu 2027 domin zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki.
Haka kuma, za a gudanar da zaben gwamna da na majalisun jihohi a ranar 6 ga Fabrairu 2027, tare da fara yakin neman zabe daga watan Agusta da Satumba 2026.
Tinubu ya gana da gwamnonin APC
An ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ganawar sirri da gwamnonin APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Taron ya samu halartar gwamnoni da dama ciki har da Hope Uzodimma na Imo, Inuwa Yahaya na Gombe da Babagana Zulum na Borno da sauransu.
Shugaban kasa ya sake jaddada goyon bayansa ga amfani da zaben kai tsaye ko tsarin sulhu wajen zaben ‘yan takarar jam’iyya.
Asali: Legit.ng

