Sheikh Dahiru Bauchi ya ziyarci Shugaban Najeriya Buhari a Villa
Dazu nan labari ya zo mana cewa babban Malamin nan da ake ji da shi a Duniya watau Shehi Dahiru Usman Bauchi ya ziyarci Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a babban Birnin Tarayya Abuja.
Sheikh Dahiru Bauchi ya kai wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara ne a fadar Shugaban kasa a yau Lahadin nan. Shehin Malamin da Tawagar sa ne dai su ka gana da Shugaban kasa a Fadar Aso Rock da ke Abuja.
Kawo yanzu dai ba mu san abin da babban Malamin na Darikar Tijjaniyyah ya tattauna da Shugaban kasar ba. Buhari Sallau ne ya fitar da hotunan ganawar jim kadan bayan shugabannin biyu sun hadu yau dinnan da rana.
KU KARANYA: Ban da wata manufar Musulunci a Najeriya inji Shugaba Buhari
Bajimin Malamin wanda Jagora ne na Mabiya ‘Darikar Tijjaniya a Najeriya da ma daukacin Afrika ya saba kira a zauna lafiya a Najeriya ba tare da nuna banbanci ba. Ba kasafai bane dai Malamin ya saba zama da Shugabannin kasar.
Kwanan nan dai kun ji cewa fitaccen Malamin addinin nan Ahmad Gumi ya ba mutanen Najeriya shawara game da shugabanci inda ya gargadi jama’a cewa masu kwadayin mulki za su yi da-na-sani.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng