Hankalin Iyalan Mutum 416 da Boko Haram Ta Sace Ya Tashi yayin da Wa'adi Ya kusa Cika
- Iyalan mutane 416 da aka sace a Ngoshe, Borno na cikin tsananin fargaba bayan wa’adin awa 72 da ‘yan ta’adda suka bayar
- ‘Yan ta’addan Boko Haram sun fitar da bidiyo inda suka bukaci kudin fansa na N5bn tare da barazanar cutar da wadanda aka kama
- Majalisar Dattawa ta bukaci hukumomin tsaro su gaggauta ceto wadanda akasari mata, yara da tsofaffi ne da ƴan ta'addan suka sace
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Iyalan mutane 416 da aka sace daga garin Ngoshe a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno sun bayyana irin azabar da suka sha lokacin da ‘yan ta’adda suka kai masu hari.
An sace mutanen ne a ranar 3 ga Maris, 2026 kuma galibinsu mata ne, yara da kuma tsofaffi, sannan suka tafi dawa da su, kuma har yanzu suna cikin kuncin rashin sanin halin da ake ciki.

Kara karanta wannan
Majalisa ta dauki mataki kan hare haren Boko Haram da suk kashe manyan sojojin Najeriya

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wannan na zuwa ne bayan Majalisar Dattawa ta bukaci hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa domin ceto dukkanin mutanen da aka sace.
'Yan Boko Haram sun yi barazana
Punch ta wallafa cewa a wani bidiyo, ‘yan ta’addan sun bukaci a biya su N5bn, tare da bayar da wa’adin awa 72. Sun kuma yi barazanar kashe wadanda suka kama idan ba a biya ba cikin lokaci.
Kungiyar matasan Borno ta Kudu (BOSYA) ta roki Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima, Gwamna Babagana Zulum da attajirai ciki har da Aliko Dangote da su taimaka wajen ganin an kubutar da mutanen.
Sanata Mohammed Ali Ndume ya shaida wa Majalisar Dattawa cewa maharan sun sake kira tare da gargadin cewa za su kashe mutanen idan ba a dauki mataki nan take ba.
Ya roki gwamnati ta kara kokari domin ceto su cikin gaggawa domin ceto su daga cikin halin kunci da suka shiga a hannun Boko Haram.

Kara karanta wannan
Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari
Borno: Mazauna Ngoshe na cikin tashin hankali
A gefe guda, wani dattijo a Ngoshe, John Gwoma, ya ce har yanzu ba su da tabbacin abin da ke faruwa da ‘yan uwansu tun bayan wancan bidiyo da ƴan ta'addan suka fitar.
Ya ce suna jin labarai ne kawai daga kafafen sada zumunta, ba su san wanda ke tattaunawa da ‘yan ta’addan ba,saboda haka ba su san komai ba.
Wani uba, Yakubu Bitrus, ya ce ya tsira da kyar yayin harin, amma dansa ya fada hannun ‘yan ta’addan. Tun daga lokacin bai sake jin labarinsa ba.

Source: Twitter
Ita ma Aisha Ibrahim ta ce suna cikin tsananin tsoro kan kanwarta matashiya da aka sace, tana mai cewa suna tsoron ƴan ta'addan za su iya aurar da ita da karfi.
Wani masani kan harkokin jama’a, Dakta Musa Usman Konduga, ya ce bukatar kudin fansa da barazanar da ‘yan ta’addan suka yi lamari ne mai sarkakiya da ya kamata a yi hankali wajen tunkararsa.

Kara karanta wannan
Yadda sojoji da tsohon minista suka raba miliyoyin Naira don kifar da gwamnatin Tinubu
A cewarsa, biyan kudin fansa na iya karfafa ‘yan ta’adda, domin zai ba su damar kara sayen makamai.
Boko Haram sun sace mazauna Borno
A baya, mun wallafa cewa ƙungiyar Boko Haram ta bayar da wa’adin sa’o’i 72 tare da barazana kan mutane 416 da ta yi garkuwa da su bayan kwashe su daga Ngoje.
'Yan ta'addan sun yi barazanar rarraba su zuwa wurare daban-daban idan ba a biya bukatunta da ta zayyana wa gwamnati ba, kuma za a iya rasa su har abada.
Boko Haram ta yi wa gwamnati taƙama, inda ta ƙalubalance ta a aiko dakaru sun zo su kwaci mutanen idan an isa, tare da bayyana cewa a shirye ta ke wajen tunkarar sojoji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng