Banbarakwai: ‘Yar sandan Najeriya ta gudu bayan ta caccakawa mijinta wuka

Banbarakwai: ‘Yar sandan Najeriya ta gudu bayan ta caccakawa mijinta wuka

Wata ‘yar sandan Najeriya, Folake Ogunbodede, mai mukamin saja, dake aiki a ofishin hukumar ‘yan sanda dake Ipaja a jihar Legas, ta cika wandonta da iska bayan caccakawa mijinta wuka a gidansu dake unguwar Apaja a garin Legas.

Wani makwabcin gidan su Folake ya shaidawa jaridar Vanguard cewar ma’auratan sun samu sabani ne da safiyar ranar Asabar, amma mijin ya fice ya bar gidan domin gudun barkewar wani rikicin tsakaninsu.

Folake ta gargadi mijin nata a kan cewar kar ya dawo gidan, amma tunda bashi da wani wurin da zai kwana sai ya dawo gidan bayan dare ya yi nisa bisa tunanin cewar matar tasa ta huce, amma duk da haka yana shigowa gidan Folake ta fara caccaka masa wuka.

Banbarakwai: ‘Yar sandan Najeriya ta gudu bayan ta caccakawa mijinta wuka
‘Yar sandan Najeriya ta gudu bayan ta caccakawa mijinta wuka
Asali: Depositphotos

Majiyar ta kara da cewar ba don makwabta sun kawo agaji ba da Folake ta kashe mijinta, Taiwo, don ko lokacin da jama’a suka isa gidan yana kwance cikin jini ko motsi ba ya yi.

DUBA WANNAN: Dakarun soji sun yiwa 'yan Boko Haram kisan kiyashi, duba hotunan gawar su

Yanzu haka dai Folake ta cika wandonta da iska, yayin da Taiwo ke can kwance asibiti inda ake kokarin ceto rayuwar sa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Legas, CSP Chika Oti, ya yi alkawarin tuntubar jaridar Vanguard bayan an kira shi domin jin tab akin hukumar ‘yan sanda. Sai dai har ya zuwa lokacin da aka kamala hada wannan rahoto bai tuntubi jaridar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel