Idan har Sule Lamido ya zama Shugaban kasa; zai hada kan 'Yan Najeriya – Jonathan

Idan har Sule Lamido ya zama Shugaban kasa; zai hada kan 'Yan Najeriya – Jonathan

- Dr. Jonathan na sa rai Jam’iyyar PDP ta lashe zaben 2019 a Najeriya

- Goodluck Jonathan yace Sule Lamido ya cancanci mulkin kasar nan

Idan har Sule Lamido ya zama Shugaban kasa; zai hada kan 'Yan Najeriya – Jonathan
Jonathan ya yabawa aikin da Sule Lamido yayi a baya
Asali: UGC

Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gana da daya daga cikin ‘Yan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP Sule Lamido a gidan sa da ke Garin Yenagoa a Bayelsa. Jonathan ya kuwa yabawa tsohon Gwamnan na Jigawa.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa tsohon Shugaban na Najeriya ya gana da kwamitin yakin neman zaben Sule Lamido jiya a gidan sa inda yace ba shakka idan Sule ya samu tikitin PDP na 2019 zai gyara Najeriya domin kuwa ya san aiki.

KU KARANTA: Sanata David Mark ya ziyarci tsohon Shugaban kasa IBB

Goodluck Jonathan wanda ya ke sa rai PDP za ta lashe zaben 2019 yace Sule Lamido zai hada kan ‘Yan Najeriya idan ya samu mulki. A cewar Jonathan, kan mutanen Najeriya ya rabu matuka a wannan lokaci na da Shugaba Buhari yake mulki.

Jonathan yace a 2011 lokacin da yake yi wa kowane Gwamnan Arewa wahala ya soki Buhari, Sule Lamido ya kan jajirce a kan bakan sa. Tsohon Shugaban kasar yace Sule Lamido ‘Dan siyasa ne mai akida kuma wanda ya san tarihin kasa.

Tsohon Gwamnan ya dai bayyanawa Goodluck Jonathan cewa yana da Muradin tsayawa takarar Shugaban kasa a 2019 a karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP inda ya kuma godewa irin tarbar da tsohon Shugaban kasar yayi masa a Garin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel