Hormuz: Matakin Amurka da Iran Ya Ta'azzara Farashin Fetur a Duniya, Gangan ta Haura $100
- Farashin man fetur a kasuwar duniya na kara hawa bayan sababbin matakan da Amurka da Iran suka ɗauka kan mashigar ruwan Hormuz
- A yanzu haka, farashi ya kafa nawa zuwa sama da Dala $106 kan kowace ganga sakamakon tashin hankali tsakanin Amurka da Iran
- Donald Trump ya ce babu jirgin ruwa da zai wuce ta Hormuz sai da izinin rundunar ruwan Amurka, ita kuma Iran ta kafa ta tsare a tekun
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States of America – Farashin danyen mai ya yi tashin gwauron zabo bayan rikicin da ke kara kamari tsakanin Amurka da Iran a mashigar ruwan Hormuz, wuri mai muhimmanci wajen jigilar makamashi na duniya.
Wannan tashin hankali ya biyo bayan cafke jiragen kasuwanci da bangarorin biyu suka yi, abin da ya kara dagula al’amura a yankin da ke fama da rikicin.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta wallafa cewa ɗanyen man Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma’aunin farashin duniya, ya haura Dala 106 kan kowace ganga da safiyar Juma’a 24 ga watan Afrilu, 2026.
Farashin fetur ya tashi saboda Iran da Amurka
Wannan ya nuna karin kusan 5% idan aka kwatanta da ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026 lokacin da farashin ya zarce Dala 100 a karo na farko cikin makonni biyu.
A lokaci guda, kasuwannin hannayen jari na Amurka sun yi kasa. Ma’aunin S&P 500 ya sauka da 0.41%, yayin da Nasdaq Composite ya ragu da 0.89%, alamar yadda kasuwanni ke nuna damuwa kan rikicin.
Mashigar Hormuz na daukan 1/5% na danyen mai da iskar gas da ake jigila a duniya, inda ake dakon su daga ƙasashe daban-daban.
Amma yanzu zirga-zirga ta tsaya cak, yayin da Iran ke neman ikon tantance jiragen da za su wuce, Amurka kuma ke hana harkokin kasuwancin ruwa na Iran.
Amurka ta ɗauki mataki kan Hormuz
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya umarci rundunar ruwan kasarsa da ta lalata duk wasu jiragen Iran da ke kokarin shimfida nakiyoyi a mashigar ruwan.
Wannan umarni ya zo ne bayan Ma’aikatar Tsaron Amurka ta sanar da kwace wani jirgin dakon mai da ake zargin na Iran ne karo na biyu cikin kasa da mako guda.
Trump ya kara da cewa babu wani jirgi da zai shiga ko fita daga mashigar ba tare da amincewar rundunar ruwan Amurka ba.

Source: Getty Images
A cewarsa:
“An rufe wurin sosai har sai Iran ta amince da yin yarjejeniya.”
A bangare guda, rundunar IRGC ta Iran ta sanar da cafke wasu jiragen ruwa biyu na kasashen waje, tana mai zargin sun karya dokokin tsaro ta hanyar aiki ba tare da izini ba da kuma tangardar na’urorin kewayawa.
Sai dai gwamnatin Girka ta musanta cewa an kama daya daga cikin jiragen nata, tana cewa har yanzu yana karkashin kulawar kyaftin dinsa.
Iran na kara shirin yaƙi
A baya, mun wallafa cewa rundunar sojin Iran ta ce tana cikin cikakken shirin ko-ta-kwana, tana jiran duk wani hari daga dakarun kasar Amurka.
Ta bayyana cewa za ta mayar da martani ta hanyar kai hari nan take kan wuraren da aka riga aka tsara idan aka auka mata ta kowace fuska yayin tsagaita wutar.
Wannan na zuwa ne bayan kalaman Donald Trump kan tsawaita tsagaita wuta da kuma ci gaba da sa takunkumi a kan jiragen ruwan Iran da ke bi ta mashigar Hormuz.
Asali: Legit.ng


