Kiwon lafiya: Sirrin shan lemon Citta da Kokomba

Kiwon lafiya: Sirrin shan lemon Citta da Kokomba

Kokomba na matukar taimakawa jiki ta hanyoyi da dama, kamar taimakon idanu da kuma sinadaran dake taimakawa wajen narkar da abinci. Kazalika tana dauke da sinadarai masu yawa da jiki ke bukata a kullum.

Citta ma na taka muhimmiyar rawa wajen rage teba da rage matsalar hawan jini.

Hadin lemon Kokomba da citta wuri guda zai karawa jiki kyau da lafiya ta hanyar rage teba da zazzage katon tumbi.

Yadda za a hada su;

A samu danyar Citta, a fere ta sannan a yayyanka ko a daka ta

A samu Kokomba guda daya a wanke sannan a yayyanka ta

A samu ruwa kofi daya, sai a zuba cikin na'urar malkade ta gida (blender) tare da Citta da Kokomba aka fere kuma aka yayyanka.

Kiwon lafiya: Sirrin shan lemon Citta da Kokomba
Lemon Citta da Kokomba
Asali: Depositphotos

Ana iya sha haka ko kuma a bar shi ya yi sanyi.

Yawan shan wannan hadin lemo zai taimaka wajen karawa jiki lafiya ta hanyar inganta sinadaran jikin mutum dake narka abinci da kuma rage matsalar hawan jini.

Masan na alakanta teba ko katon tumbi da rashin ingancin hanya ko sinadaran dake sarrafa abincin da mutum ya ci.

DUBA WANNAN: Yadda zaku yi maganin amosanin ka

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar Gwamnan jihar Washington ta kasar Amurka, Jay Islee, ya nada wani dan asalin Najeriya, Edirin Okolok, a matsayin sabon alkalin kotun lardin Snohomish County bayan ritayar alkalin kotun, George Bowden.

Okoloko ya shafe shekaru 13 yana aiki a sashen cin mutuncin yara, manya da mata a kotun ta lardin Snohomish County.

Nadin Okoloko ya biyo bayan irin nasarar da ya samu a laifukan da ya jagoranci gurfanar da wadanda suka aikata su yayin da yake aiki a sashen gurfanar da masu laifi a kotun ta Snohomish County.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel