Latest
Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa, miyagun 'yan ta'adda da ake zargi da ta'addancin fashi da makami, sun hallaka wani babban Limamin kauye Kwara da ke karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa.
Za ku ji yadda Atiku ya zakulo kwararrun Lauyoyin da ake ji da su wanda Dr. LIVY UZOUKWU LL.B, LL.M, LLD, SAN, OON shi ne Jagoransu. Kuma har da Abokin takarar Atiku a PDP yana cikin Lauyoyinsa a Kotu.
Ko shakka ba bu an haife ta a ranar 21 ga watan Afrilun 1926, inda a ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilun 2019, sarauniyar Ingila Elizabeth Alexandra Mary ta biyu, ta yi murnar cikar ta shekaru 93 da bayyana a idon duniya.
Jami'an hukumar hana fasakauri sun dakume wata mata 'yar asalin kasar Najeriya a harabar filin jirgin sama na birnin Hong Kong da ke kasar Sin dauke da fiye da rabin kilo na hodar iblis kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Masarautar jihar Zamfara ta nemi gafarar rundunar hukumar sojin saman Najeriya sakamakon zargin ta da kashe al'ummar jihar wadanda ba su ji ba kuma ba su gani yayin wani luguden wuta da ta zartar wajen yakar 'yan ta'adda.
Okeigbo yar asalin jihar Abia, ta haifi yara maza 3 da kuma mata 2 a ranar 17 ga watan Afrilu bayan da akayi mata aiki. Da take zantawa da yan jarida matar tace, tana matukar godiya ga Allah da yayi mata wannan kyauta inda ta kara
A yau Asabar dinnan ne wasu da ake zargin barayi ne, suka kashe limamin kauyen Kwara, dake karamar hukumar Kiyawa, cikin jihar Jigawa, hukumar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwan lamarin. Mai magana da yawun hukumar 'ya...
Babban limamin masarautar Ebira, Alhaji Musa Galadima, ya rasu a safiyar ranar Juma'a, 19 ga watan Afrilu, 2019 yana mai shekaru 98 a duniya. NAN ta bada rahoto.
Shugaban 'yan ta'addar da suka addabi al'ummar jihar Zamfara ya bayyana cewa za su cigaba da kashe mutane a jihar, tunda har gwamnatin tarayya ta cigaba da aiko da jami'an tsaro domin dauki ba dadi...
Masu zafi
Samu kari