Yanzu - yanzu: An kashe Limami a jihar Jigawa

Yanzu - yanzu: An kashe Limami a jihar Jigawa

- Wasu da ake zargin barayi ne sun kashe wani limami a jihar Jigawa

- Barayin sun dauke kudin gonar da limamin ya sayar akan kudi naira dubu dari hudu

- Bayan sun kashe shi sun bi iyalan shi duka suka zane su

A yau Asabar dinnan ne wasu da ake zargin barayi ne, suka kashe limamin kauyen Kwara, dake karamar hukumar Kiyawa, cikin jihar Jigawa, hukumar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwan lamarin.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar, SP Abdu Jinjiri, shine ya fadawa kamfanin dillacin labarai na Najeriya, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 1:30 na dare.

Jinjiri ya ce marigayin mai suna, Al-Sheikh Idris Musa, mazaunin garin Kwara, barayin sun kai masa hari a gidansa bayan ya sayar da gonarsa akan kudi naira dubu 400, ga wani kamfanin gine-gine da ke jihar.

Yanzu - yanzu: An kashe Limami a jihar Jigawa
Yanzu - yanzu: An kashe Limami a jihar Jigawa
Asali: Depositphotos

Ya ce wadanda ake zargin sun yi ta dukan marigayin da itace, wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Jami'in ya kara da cewa wadanda ake zargin sun dauki kudin da marigayin ya sayar da gonar ta sa, naira dubu dari hudu.

A cewarsa, wadanda ake zargin bayan kashe marigayin, sun daki matanshi da 'ya'yanshi.

"Ana tsammanin cewa an yi cinikin gonar a gaban wadanda ake zargin, sai dai har yanzu ba a san su waye ba.

KU KARANTA: 'Yan bindigar jihar Zamfara sun aika da wani sako ta wayar salula

"Munn dauki iyalan marigayin da barayin suka daka munn kai su asibiti mafi kusa domin karbar magani," in ji Jinjiri.

Ya kara da cewa sun bar gawar marigayin ga iyalanshi domin ayi masa sallah a binne shi.

Ya ce, yanzu haka 'yan sanda sun fara gabatar da bincike akan lamarin, kuma za su yi kokari wajen ganin sun kama wadanda ake zargin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel