Abubuwa 5 game da Sarauniyar Ingila yayin da ta cika shekaru 93 a duniya

Abubuwa 5 game da Sarauniyar Ingila yayin da ta cika shekaru 93 a duniya

Ko shakka ba bu an haife ta a ranar 21 ga watan Afrilun 1926, inda a ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilun 2019, sarauniyar Ingila Elizabeth Alexandra Mary ta biyu, ta yi murnar cikar ta shekaru 93 da haihuwa tare da bayyana a idon duniya.

A yayin da Sarauniyar Ingila ta shafe kwanaki 33,962 a doron kasa, ga wasu muhimman ababe biyar da ta kafa a tarihin rayuwar ta da ba ku sani ba;

Bayan cin gajiyar masarautar Ingila a ranar 6 ga watan Fabrairun 1952, Sarauniyar Ingila ta ci zamani da Firai Ministoci 14 na kasar Ingila. Kazalika Sarauniyar Ingila ta yi zamani da shugabannin kasar Amurka 11 cikin 12 da kasar ta yi a tarihin duniya.

Sarauniyar Ingila

Sarauniyar Ingila
Source: UGC

Yayin da ta kafa tarihi a duniya na kasancewar ta Sauraniya mafi jimawa a kan gadon mulki da ta shafe shekaru 67 da kwanaki 74 a bisa gadon Sarauta, ta rattaba hannu kan fiye da dokoki 3,500 na kasar Birtaniya.

Ta na da tarin kadara ta dabbabo musamman Karnai da kuma Dawaki da ta ci gajiyar su wajen mahaifin ta, Sarki George na hudu da ya riga mu gidan gaskiya a shekarar 1952. Ta kuma mallaki wasu nau'ikan dabbobi daban-daban.

KARANTA KUMA: Hukumar 'yan sanda ta cafke makamai a ofisoshin jam'iyyar APC da PDP a Kano

Sarauniyar Ingila ta na masaniya daidai gwargwado a kan mu'amala da kayayyaki na fasahar zamani kasancewar ta tsohuwar mai gyaran Mota a lokacin yakin duniya na biyu.

Duk da cewa doka ba ta shar'an ta mata ba, Sarauniyar Ingila ta wajabtawa kanta biyan haraji a kan wasu kadarori da ta mallaka biyo bayan wasu zantukan guna-guni na Talakawan ta.

KARANTA KUMA: Hukumar 'yan sanda ta cafke makamai a ofisoshin jam'iyyar APC da PDP a Kano

Ta aika da sakon farko ta hanyar yanar gizo wato email a shekarar 1976, inda ta aike da wani sakon zuwa ga masu ziyarar duniyar wata; Niel Armstrong da kuma Buzz Aldrin a shekarar 1969. Ta rubuta sakon farko a shafin ta na sada zumunta na Twitter a shekarar 2014.

Bikin nadin Sarautar Sarauniyar Ingila, shi ne na farko da aka watsa a gidajen Talabajin a shekarar 1953.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel