An kashe babban Limami a jihar Jigawa, an yi masa fashi na N400,000

An kashe babban Limami a jihar Jigawa, an yi masa fashi na N400,000

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa, miyagun 'yan ta'adda da ake zargi da ta'addancin fashi da makami, sun hallaka wani babban Limamin kauye Kwara da ke karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Abdu Jinjiri, yayin ganawar sa da manema labarai cikin birnin Dutse ya bayar da shaidar cewa, ta'addancin ya auku ne da misalin karfe 1.30 na daren ranar Asabar da ta gabata.

An kashe babban Limami a jihar Jigawa, an yi masa fashi na N400,000

An kashe babban Limami a jihar Jigawa, an yi masa fashi na N400,000
Source: Twitter

Jinjiri ya ce maharan sun hallaka Al Sheikh Musa mai shekaru 65 a gidan sa ta hanyar bugun dawa bayan ya sayar da wata gonarsa a kan zunzurutun kudi na Naira dubu dari hudu. Sun yi awon gaba da dukiyar kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Ba ya ga hallaka babban Limamin, 'yan ta'addan kamar yadda babban jami'in dan sandan ya bayyana sun kuma lakadawa iyalan sa dukan tsiya inda ya cika a yayin yunkurin ba su kariya tare da tseratar da su.

KARANTA KUMA: Hukumar NDLEA ta cafke Mutane 2 da hodar Iblis a jihar Kano

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, 'yan ta'adda a ranar Juma'a bayan kashe mutane biyu sun kuma yi garkuwa da Mutane uku a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel