Zaratan Sojoji sun kashe yan bindiga 6, sun kama dakatai 2 masu aikin leken asiri (Hotuna)

Zaratan Sojoji sun kashe yan bindiga 6, sun kama dakatai 2 masu aikin leken asiri (Hotuna)

Dakarun rundunar Sojan kasa dake aikin tabbatar da tsaro a jahar Zamfara na Operation Harbin Kunama III sun samu nasarar dakile wasu yan bindiga a kauyukan Kirsa da Sunke dake cikin karamar hukumar Anka ta jahar Zamfara.

Kaakakin rundunar Sojan kasa, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu, inda yace Sojoji sun yi musayar wuta da yan bindigan, inda suka kashe mutane guda shida, tare da kwace bindigu guda guda kirar AK47 da babura 2.

KU KARANTA: Basu ji ba, basu gani ba: Dansanda ya tattake mutane 9 da mota, ya jikkata 32 a Gombe

Zaratan Sojoji sun kashe yan bindiga 6, sun kama dakatai 2 masu aikin liken asiri (Hotuna)
Baburan
Asali: Facebook

Haka zalika, Sojojin sun yi wata arangama da yan bindiga a ranar 20 ga watan Afrilu a kayukan Doka da Mutu dake cikin karamar hukumar Gusau, inda aka kwashe sama da awanni biyu ana dauki ba dadi.

Sai dai Kanal Sagiru yace sun zaratan Sojojin Najeriya sun yi amfani da dabarun yaki wajen kwantar da yan bindigan, tare da kashe wasu daga cikinsu, yayin da sauran suka ranta ana kare, sa’annan Sojojin sun kama masu ma yan bindigan leken asiri su 18, daga ciki har da dakatan kauyukan Doka da Mutu.

Zaratan Sojoji sun kashe yan bindiga 6, sun kama dakatai 2 masu aikin liken asiri (Hotuna)
Makamai
Asali: UGC

Daga cikin kayan da suka kwato akwai babura guda 3, bindigun toka guda 2 da kuma adduna 2. Daga karshe kwamandan Operation Harbin Kunama, Manjo Janar Hakeem Oladapo Otiki ya jinjina ma Sojojin, sa’annan ya bukaci da kada su saurara ma yan bindiga a duk inda suka gansu.

Haka zalika ya nemi jama’a dasu cigaba da bada hadin kai ga jami’an tsaro ta hanyar jiyar dasu bayanan sirri game da duk wasu yan bindiga, musamman a jahohin Zamfara Katsina, Kebbi da Sokoto don kawo karshen ayyukan yan bindigan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel