Malaman Kungiyar addinin Izala sun tafi kasashen waje

Malaman Kungiyar addinin Izala sun tafi kasashen waje

Mun samu labari cewa shugabannin kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa’ikamatus Sunnah na JIBWIS wanda aka fi sani da Izala sun harba zuwa kasar Amurka jim kadan bayan babban zaben 2019

Jaridar Desert Herald ta soki ziyarar da Malaman Izala karkashin jagorancin Abdullahi Bala Lau su ka kai zuwa Amurka a daidai lokacin da Mabiyansu ke cikin wani mawuyacin hali a kusan kowane bangare na Najeriya.

Idan ba za ku manta ba, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya nuna goyon bayansa ga a fili ga takarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019, yayin da Sakataren kungiyar watau Kabiru Gombe ya rika caccakar ‘Dan takarar PDP.

Jaridar ta zargi shugabannin wannan kungiyar addini na reshen Kaduna da karbar kudi daga hannun jam’iyyar APC wanda ya sa su ka rika sukar Abokin takarar shugaba Buhari watau Alhaji Atiku Abubakar babu kaukautawa.

KU KARANTA: Sarakunan Zamfara sun nemi sojin Najeriya su yafe masu

Malaman Izala sun tafi kasashen waje yayin da ake cikin mawuyacin hali

Muhammad Kabir Haruna Gombe a ofishin Majalisar dinkin Duniya
Source: UGC

Desert Herald tana zargin Sheikh Bala Lau da kuma Muhammad Kabir Haruna Gombe da karbar sama da Naira Miliyan 500 da kuma manyan motoci daga hannun wasu gwamnonin APC irin su gwamnan jihar Adamawa Jibrila Bindow.

An kuma zargi manyan kungiyar da karbar motoci daga hannun wani gwamnan Arewa maso yamma a lokacin da ake yakin zabe. Jaridar tace Malaman kungiyar sun buge ne da sanya tufafin takama da motoci a maimakon aikin addini.

Rahotannin su ke cewa Bala Lau ya zabi ya tafi kasar Amurka ne a lokacin da Musulmai ke fama da ‘dan karen talauci da yunwa. An dai ga Kabir Gombe cikin hotuna yayin da yake shakatawa a wurare dabam-dabam a cikin kasar ta Amurka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel