Fada Ya Barke tsakanin Kungiyoyin 'Yan Bindiga a Zamfara, an Kashe Hatsabibon Jagora

Fada Ya Barke tsakanin Kungiyoyin 'Yan Bindiga a Zamfara, an Kashe Hatsabibon Jagora

  • An samu hargitsi wanda ya jawo barkewar fada tsakanin wasu kungiyoyin 'yan bindiga a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Fadan da ya barke ya jawo an hallaka wani jagoran 'yan bindiga mai suna Kachalla Haire tare da mayaka da dama
  • Mutanen yankin sun nuna jin dadinsu game da kisan da aka yi wa Kachalla Haire saboda yadda ya dade yana jagorantar ayyukan ta'addanci

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - An bayar da rahoton kashe wani shahararren jagoran ’yan bindiga da aka sani da Kachalla Haire, wanda aka fi sani da “Mala’ikan Mada,” a jihar Zamfara.

An kashe Kachalla Haire ne yayin wani kazamin fadan nuna ƙarfi tsakanin kungiyoyin ’yan bindiga masu gaba da juna a jihar Zamfara.

An kashe jagoran 'yan bindiga a Zamfara
Jagoran 'yan bindiga a Zamfara, Kachalla Haire Hoto: Shehu Umar
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

"Akwai su a gwamnati": Gwamna Radda ya tona masu taimakon 'yan bindiga a Katsina

Yadda aka kashe jagoran 'yan bindiga

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma'a 8 ga watan Mayu, 2026, sakamakon rashin jituwa da aka samu tsakanin kungiyoyin ’yan bindiga kan rabon kayayyaki da abubuwa masu daraja na wani shugaban ƙungiyar da ya mutu.

Majiyoyin sun ce takaddamar ta rikide zuwa mummunan fadan harbe-harbe tsakanin rukunonin masu gaba da juna, wanda ya kai ga rahoton kisan Haire da wasu mayaka da dama.

An bayyana cewa Haire ya dade yana cin karensa ba babbaka a yankin Mada da ke ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara, kuma an dade ana alaƙanta shi da jerin hare-hare, kisan kai, garkuwa da mutane, da sauran ayyukan ta’addanci a fadin al’ummomin da abin ya shafa.

Mutane sun ji dadin kisan jagoran 'yan bindiga

Mazauna wasu sassan yankin sun nuna jin daɗinsu game da wannan cigaban, inda suka siffanta shugaban ’yan bindigan da ya mutu a matsayin ɗaya daga cikin manyan mutanen da ke da alhakin shekaru da dama na rashin tsaro da fargaba a yankin.

Kara karanta wannan

Shin da gaske 'yan bindiga sun kashe mutane a wurin jana'iza a Plateau? Gaskiya ta bayyana

An kashe Kachalla Haire a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ana ganin wannan cigaba na baya-bayan nan a matsayin wani ɓangare na ƙaruwar rarrabuwar kawuna da takaddamar shugabanci a tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga da ke gudanar da ayyukansu a faɗin Zamfara, Katsina, da sassan yankin Arewa maso Yamma.

Hukumomin tsaro na ci gaba da ƙarfafa hare-hare, ayyukan tattara bayanan sirri, da hare-hare ta sama da ƙasa kan maboyar masu laifi domin ruguza hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda da na ’yan bindiga da ke gudanar da ayyuka a yankin.

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa yan bindiga dauke da makamai sun kai hari wani sansanin rundunar ƴan sanda masu kwantar da tarzoma (PMF) a jihar Kwara.

'Yan bindigan sun kai harin ne a yankin Tenebo, da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, inda suka kashe aƙalla jami’ai uku tare da raunata wasu guda biyu.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun afka wa sansanin ne da dambin yawa, inda wasu daga cikinsu suke kan babura yayin harin da suka kawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng