Allah ya yiwa limamin kasar Ebira, Alhaji Musa Galadima, rasuwa

Allah ya yiwa limamin kasar Ebira, Alhaji Musa Galadima, rasuwa

Babban limamin masarautar Ebira, Alhaji Musa Galadima, ya rasu a safiyar ranar Juma'a, 19 ga watan Afrilu, 2019 yana mai shekaru 98 a duniya. NAN ta bada rahoto.

Galadima wanda ya yi shekaru 55 matsayin limamin garin ya mutu ne a wani asibiti dake birnin tarayya Abuja kuma an yi jana'izarsa a garin Okene bisa da koyawar addinin Musulunci.

The state governor, Alhaji Yahaya Bello, described Galadima’s death as painful in a statement in Lokoja.

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahya Bello, ya bayyana radadin da ya ki yayinda ya samu labarin mutuwar Galadima inda yace:

"Ya kasance mutum mai kankan da kai, mai natsuwa kuma malamin da'awa wanda iliminsa ya ketare Najeriya."

"Marigayin ya kasance mai tsoron Allah, mai tawalu'u da kuma biyayya ga shugabanni musamman sarakunan gargajiya"

Ya yi kira ga sauran malaman adini suyi koyi da rayuwar marigayin.

Gwamna Bello ya mika sakon ta'azziyarsa ga mai martaba sarkin kasar Ebira, Ohinoyi of Ebiraland, Alhaji Ado Ibrahim, iyalan marigayin, 'yayansa, abokai, dalibai da daukacin al'umma kan rashin limamin.

Ya roki Allah ya gafarta masa kura-kuransa kuma ya saka masa da gidan Aljannan. Amin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel