Kuma dai! Yan bindiga sun sake kashe mutane 10 a jahar Katsina

Kuma dai! Yan bindiga sun sake kashe mutane 10 a jahar Katsina

Wasu gungun mahara yan bindiga sun bude ma jama’n mazauna kauyen Sherere dake cikin karamar hukumar Kankara ta jahar Katsina, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane goma, tare da raunata wasu da dama.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun afka ma kauyen ne dayawansu akan babura kirar Boxer, inda suka shiga harbin mai kan uwa da wabi, daga bisani kuma suka bi duk wasu shaguna da ababen hawa suna banka musu wuta.

KU KARANTA: Watsi da hadisin Annabi ya janyo ma wani makwabci shiga tsaka mai wuya

Wani mazaunin kauyen, Dikko Shere ya shaida ma majiyarmu cewa a yanzu basu ma iya fita daga gidajensu don gudanar da jana’iza akan mamatan da yan bindigan suka kashe saboda tsoron kada su afka musu yayin da suke Sallar.

“Zuwa yammacin jiya, mun tattaro gawarwaki guda bakwai, amma da safiyar nan, mun sake gano wasu gawarwaki guda uku, wanda hakan ya kawo jimillan gawarwakin da muka iya ganowa zuwa goma.

“A yanzu haka mun kasa binnesu saboda kowa ta kansa yake, jama’a da dama suna kwashe iyalansu suna gudun hijira zuwa wasu yankunan da suke ganin zasu tsira.” Inji shi.

A yan kwanakin nan matsalar hare haren yan bindiga yayi kamari a jahar Katsina, inda bai wuce sati biyu da suka gabata ba sai da yan bindiga suka kai ma wani kauye mai suna Tsamiyar Jino hari, inda suka kashe mutane da dama.

Sai dai ana ganin hakan baya rasa nasaba da nasarar da dakarun Sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro suke samu a yakin da suke yi da yan bindiga a jahar Zamfara, don haka sai yan bindigan suke komawa jahar Katsina.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel