Iran Ta Seta Komai, Ta Gargadi Amurka game da Jiragen Ruwanta a Yakin da Ake Yi

Iran Ta Seta Komai, Ta Gargadi Amurka game da Jiragen Ruwanta a Yakin da Ake Yi

  • Rundunar IRGC ta Jamhuriyar Musulunci a Iran ta yi barazanar kai munanan hare-hare kan sansanonin Amurka da jiragen ruwa.
  • Iran ta yi wannan gargadi ne ga kasar idan ta kai hari kan tankokin mai ko jiragen kasuwancin kasar wanda ka iya jawo martani mai zafi
  • Rikicin Iran da Amurka tare da Isra’ila ya kara tsananta bayan hare-haren da aka kai tun watan Fabrairu, lamarin da ya haddasa martanin Tehran da rikicin mashigar Hormuz

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi gargadi mai tsauri ga kasar Amurka da kawayenta.

Kasar ta ce duk wani hari da aka kai kan tankokin man fetur ko jiragen kasuwancin Iran zai jawo mummunan martani.

Iran ta gargadi Amurka a yakin da ake yi
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Donald Trump na Amurka. Hoto: Anadolu Ajansi, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Hakan na cikin wata sanarwa da rundunar sojin ruwan IRGC ta fitar ta hannun kamfanin dillancin labarai, kamar yadda Al Jazeera ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Iran ta lalata jiragen Amurka bayan kasar ta kai mata hari a mashigar Hormuz

Barazanar Iran ga Amurka a yaki

Rundunar ta ce za ta kai “mummunan hari” kan sansanonin Amurka da jiragen ruwa na abokan gaba a yankin idan aka taba jiragen Iran.

Kwamandan rundunar sararin samaniyar IRGC, Manjo Janar Majid Mousavi, ya bayyana cewa makamai masu linzami da jirage marasa matuka na Iran suna cikin shiri tare da jiran umarnin kaddamar da hari.

A gefe guda, ma’aikatar tsaron Birtaniya ta sanar da tura jirgin yakin ruwa HMS Dragon zuwa Gabas ta Tsakiya domin shirin yiwuwar aikin hadin gwiwa da Faransa na kare jiragen ruwa masu kasuwanci a mashigar Hormuz.

Iran ta sha alwashin tarwatsa jiragen Amurka
Sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Abin da ya jawo rufe mashigar Hormuz

Rahotanni sun nuna cewa an dauko jirgin daga gabashin tekun Bahar Rum kusa da Cyprus domin kasancewa cikin shiri idan bukatar shiga aikin tsaro ta taso.

Tashin hankalin yankin ya kara tsananta ne bayan Amurka da Isra’ila sun kai hare-hare kan Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026, wanda ya jawo martanin Tehran kan Isra’ila da wasu kawayen Amurka a yankin Gulf.

Kara karanta wannan

An bankaɗo girman ɓarnar da Iran ta yi wa Amurka, abin ya wuce yadda ake faɗa

Hakan ya haddasa rufe mashigar Hormuz, daya daga cikin manyan hanyoyin safarar mai a duniya, cewar Anadolu Ajansi.

Ko da yake an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Afrilu ta hanyar shiga tsakani na Pakistan, har yanzu ba a kai ga cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya ba.

Tun daga ranar 13 ga Afrilu, Amurka ta fara kakaba takunkumin jiragen ruwa kan zirga-zirgar Iran a yankin, yayin da Shugaba Donald Trump ya ce za a dakatar da wani bangare na shirin “Project Freedom” domin dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa na kasuwanci cikin sauki.

Trump ya magantu kan raunin Iran

A wani labarin, an ji cewa shugaba Donald Trump ya bayyana cewa kasar Iran ta rasa karfin sojoji sosai a yakin da ta ke yi da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya.

Trump ya bukaci kasar ta mika wuya yana mai cewa kamata ya yi Tehran ta daga tutar zaman lafiya domin kawo karshen rikicin.

Shugaban Amurka ya ce Iran na son cimma yarjejeniya a boye duk da kalaman barazana da take yi a bainar jama’a kan rikicin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.