Bayan shekara 18 da aure, wata mata ta haifi yara 5 a jihar Kogi

Bayan shekara 18 da aure, wata mata ta haifi yara 5 a jihar Kogi

-Idan da ranka ka sha kallo! wata ta haifi yara biyar a Lokoja

-Ikon Allah yafi gaban mamaki, bayan shekara 18 ba haihuwa sai gashi Allah ya bata biyar a lokaci guda

Matar mai shekara 42 ta haifa jarirai biyar a babbar cibiyar kula da lafiya dake Lokoja bayan shekara 18 da aurenta. Wani daga cikin yan jarida wanda ya samu ganin wannan mata mai suna Uchenna Okeigbo yace ita uwar da jariran nata dai suna cikin yanayi mai kyau.

Okeigbo yar asalin jihar Abia, ta haifi yara maza 3 da kuma mata 2 a ranar 17 ga watan Afrilu bayan da akayi mata aiki. Da take zantawa da yan jarida, matar ta ce tana matukar godiya ga Allah da yayi mata wannan kyauta inda ta kara da cewa jiran da tayi na tsawon shekaru 18 bai tafi a banza ba.

Bayan shekara 18 da aure, wata mata ta haifi yara 5 a jihar Kogi

Bayan shekara 18 da aure, wata mata ta haifi yara 5 a jihar Kogi
Source: UGC

KU KARANTA:Kungiyar kare yancin dan adam ta soki CP Wakili bisa kama mataimakin gwamnan Kano

“Mawuyacin abu ne mutum ya haifi diya biyar lokaci guda,” tace. Matar tayi matukar jinjinama mijinta bisa ga goyon baya da kwarin gwiwar da yake bata na tsawon lokaci.

Mahaifin wadannan yara, James Okeigbo mai shekara 47 shima ya nuna farin cikinsa na wannan abin murna da ya samesu, inda yace hakika wannan shine babban abun farin ciki da ya taba faruwa dasu shi da matarsa.

“Ya zama dole in godewa matata na hakuri da juriya da tayi har tsawon shekara 18 ba tare da bacin rai ko fada ba. Har wa yau ba zan mance da iyalanta ba suma bisa hakurin da sukayi da kuma kara karfafa mana gwiwa a koda yaushe.”

A karshen jawabinsa ya nemi taimako daga wurin gwamnati domin ya samu damar daukar nauyin wadannan yara 5 tare da mahaifiyarsu. Kasancewar kowa ya san suna bukatar kulawa ta musamman. A matsayina na asalin dan Najeriya ina kira ga gwamnati da ta taimaka mana.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel