An cafke 'yar Najeriya da hodar Iblis a birnin Sin
Jami'an hukumar hana fasakauri sun dakume wata mata 'yar asalin kasar Najeriya a harabar filin jirgin sama na birnin Hong Kong da ke kasar Sin dauke da fiye da rabin kilo na hodar iblis kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Jaridar South China Morning ta ruwaito cewa, Matar mai shekaru 37 a duniya, ta iso birnin Sin bayan ta keto hazo daga jihar Legas ta biranen Addis Ababa da kuma Habasha.
Da ya ke dai Hausawa na cewa mara gaskiya ko a cikin ruwa sai ya yi gumi, ya sanya jami'an Kwastam suka zargi Matar inda kuwa suka cimma nasarar bankado wannan mummunar hoda yayin bincikar ta a ranar Alhamis.
Bayan gudanar da bincike a asibitin Queen Elizabeth da ke birnin Hong Kong, an samu daurin hodar Iblis mai nauyin giram 215 da ta sakaya cikin farjin ta, ba ya ga hodar mai nauyi giram 214 da ta hadidiye.
KARANTA KUMA: Zargin Kashe Kashe: Masarautar Zamfara ta nemi yafiyar rundunar sojin sama
Duka duka dai an samu hodar Iblis mai nauyin giram 550 tattare da wannan Mata, wanda darajar kudin ta ya kai kimanin Dalar Amurka 66,900.
A watan Maris na shekarar 2016 da ta gabata, an cafke wata Mata 'yar kasar Brazil mai shekaru 42 dauke da hodar Iblis mai nauyin giram 400 da ta makale cikin farjin ta.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng