Yadda ake fasa kaurin buhuhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin Najeriya a kullun

Yadda ake fasa kaurin buhuhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin Najeriya a kullun

- Wani bincike ya nuna cewa buhuhunan shinkafa miliyan 20 ne ake shigowa da su kasar Najeriya a kulla yaumin ta haramtacciyar hanya

- Abdullahi Zuru, babban manajan kamfanin Labana Rice Mills, yace shigo da shinkafa ta haramtacciyar hanya zai zamo barazana ga shirin ba da rance na babban bankin Najeriya (CBN)

- Zuru har ila yau yace fasa kauri na cigaba da shafan noman shinkafa a kasar

Babban manajan Labana Rice Mills, wani kamfani na asali mai noma da sarrafa shinkafa a jihar Kebbi, Abdullahi Zuru yayi korafi akan cigaba da ake samu wajen shigowa da shinkafa Najeriya ta haramtattun hanyoyi.

Zuru yayin da yake magana da yan jarida a Birnin Kebbi, yace hakan ya zamo barazana ga shirin ba da rance wacce babban bankin Najeriya (CBN) ta kaddamar don tabbatar da noman shinkafa a kasar.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Zuru yace kungiyar manoman shinkafa na Najeriya (RIFAAN) ta gudanar da bincike tsakanin watan Fabrairu zuwa Maris na wannan shekarar, binciken ya kuma nuna cewa fiye da buhunan shinkafa miliyan 20 ne ake shigowa dasu Najeriya ta haramtattu hanyoyi da iyaka daban daban.

Yadda ake fasa kaurin buhuhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin Najeriya a kullun
Yadda ake fasa kaurin buhuhunan shinkafa sama da miliyan 20 cikin Najeriya a kullun
Asali: Depositphotos

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kamfanin Amarava Rice Mill dake Kano tace tana son ace tana samar da shinkafa tan 500 a kowace rana daga watan Yuli, kamar yanda ta sarrafa tan 250 don bunkasa noman kasar.

Subhash Chand, mataimakin wakilin Indiya a Najeriya, ya bayyana hakan a ranar 1 ga watan Janairu, a Abuja.

A watan Disamban da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kamfanin shinkafa na miliyoyin nairori na wani dan Indiya.

Wakilin ya bada tabbacin cewa ana aiki don ganin an inganta yawan abunda ake samu zuwa tan 500 a watan Yuli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel