Matasa na iya hana mu manyan mutane fita nan da shekara 5 - Dangote

Matasa na iya hana mu manyan mutane fita nan da shekara 5 - Dangote

Shahararren dan kasuwar nan kuma mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa akwai yiwuwar cewa nan da wasu yan shekaru biyar masu zuwa matasan jihar Kano da basu da aikin yi na iya hana manyan mutane daga jihar fita koda wajen gidansu saboda za su iya zama barazana.

Jaridar Leadership Hausa ta ruwaito cewa attajirin mai arzikin ya fadi hakan ne a yayin gudanar da babban taron ci gaban jihar Kano, wanda kungiyar samar wa jihar alkibla ta KCC ta shirya a ranar Asabar da ta gabata.

An tattaro inda Dangote ke cewa: “yadda Allah ya azurta kasarmu ta Najeriya da filin noma har kashi 75 na kasar, to bai kamata a ce mutanenmu na cikin kangi na talauci ba. Don haka dole ne mu tashi tsaye wajen bunkasa harkar noma da masana’antu, domin su ne manyan hanyoyi fitar da kasa daga talauci yadda za ta samu cigaba.

“Kamar yadda kasashen duniya su ka dauki matakan ciyar da kasashensu gaba, to mu ma haka ne ya kamata mu yi.“

Matasa na iya hana mu manyan mutane fita nan da shekara 5 - Dangote
Matasa na iya hana mu manyan mutane fita nan da shekara 5 - Dangote
Asali: Getty Images

Ya kara da cewa, “irin abubuwan da su ke faruwa ya nuna haka, kamar shekara daya da rabi da ta wuce na je sallar Juma’a a Abuja na yi shiga ta doguwar riga, wacce da yawa mutane ba sa gane ni sabanin irin shigar da na saba yi ta babbar riga, amma sai wani matashi ya kyalla ido ya ce ga Dangote. Kafin lokaci kadan matasa sama da dubu sun rufe ni. Da kyar na shiga mota. Don haka dole mu dauki matakin sama wa matasa aikin yi.”

Haka kuma Dangote ya ce, “ba wani shugaba ko wani gwamna da za mu zaba wanda ba zai yiwa al’umma aiki ba, kuma dole ne wannan tafiya mu kira gwamnoninmu, musamman na Arewa mu gaya musu gaskiya, mu tunkari wannan kalubale gaba daya.”

KU KARANTA KUMA: Matasan arewa sun yi wa Tinubu wankin babban bargo kan shugabancin majalisa

Haka kuma Dangote ya sha alwashin shi da dan kasuwa dan uwansa Alhaji Abdussamadu Isiyaka Rabiu za su gina katafariyar cibiyar koyar da sana’o’i, don amfanin matasa maza da mata a Kano, za kuma su gina titi mai tsawon kilo mita tara wanda ya lalace a Sharada, wanda za su yi amfani da kudin harajinsu da su ke biya, kamar yadda a ka cimma yarjejeniya a hukumance da kuma bada tallafin biliyoyin Nairori, “don ciyar da jihar nan gaba kamar yadda ni Dangote da BUA mu ke da kudirin haka.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel