Latest
Rahoton da muke samu na nuna cewa ana cigaba da garkuwa da mutane da a hanyar Abuja zuwa Kaduna yayinda yan bindigan sukayi awon gaba da fasinjojin mota kirar Golf da safiyar Litinin, 8 ga watan Yuli, 2019.
Kwanan nan wata ta kashe ‘Danuwan ta saboda sun samu karamin rikici a kan casun biki a Kano. ‘Yan Sanda sun cafke wannan Yarinyar da ta kashe babban Yayan ta a kan abin da be kai ya kawo ba.
Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun kashe mutane da dama a kauyukan Dan Sabau, Pawwa da Makera da ke karamar hukumar Kankara na jihar Katsina a daren ranar Asabar.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Awolowo ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin da yake ganawa da manema labaru a fadar gwamnati bayan wata ganawa da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a.
Wata tsohuwa yar shekara 70, mai suna Moyo Jide, da jikokinta hudu sun rasa rayukansu a gobara da safiyar yau Asabar 6 ga watan Yuli 2019 a kauyen Biagbini dake a karamar hukumar Ese Odo dake a jihar Ondo
Rahoton kamfanin dillancin labaru ya bayyana daga cikin mutanen da yan bindigan suka sako har da kananan yara guda 3, maza 5 da kuma mata 3, wanda aka mikasu ga gwamnan jahar Zamfara a ranar Lahadi a garin Gusau.
Wasu Jihohi 12 su na fama da bashin fiye da Naira Tiriliyan 2. Gwamnonin da su ka ci wannan bashi su ne: Abdulaziz Yari, Ibrahim Gaidam, Mohammed Abubakar, Ibrahim Dankwambo da Muhammadu Bindow da sauran su.
A Ranar 7 ga Watan Yuli mu ka ji cewa Mai martaba Sarkin Hadejia ya yabawa Gwamna Badaru na bada gudumuwar fili. Musulmai sun samu kwarin gwiwar gina Makaranta watau Jami’ar JIBWIS da za ayi a Jigawa.
A wani yanayi da salo mai kama da na shirin fim, dangin amarya sun kashe wani ango tare da abokansa da suka zo kauyen Borong da ke karamar hukumar Demsa a jihar Adamawa daga jihar Borno domin daurin aure. Marigayin, Luka Yakubu,
Masu zafi
Samu kari