Yan bindigan jahar Zamfara sun sake sako mutane 11 da suka kama

Yan bindigan jahar Zamfara sun sake sako mutane 11 da suka kama

Matakin yin sulhu tsakanin yan bindiga da matasa yan sa-kai da gwamnan jahar Zamfara Bello Matawalle ya dauki gabaran yin a cigaba da samun tagomashi yayin da wata kungiyar yan bindiga ta sako mutane goma sha daya da take rike dasu.

Rahoton kamfanin dillancin labaru ya bayyana daga cikin mutanen da yan bindigan suka sako har da kananan yara guda 3, maza 5 da kuma mata 3, wanda aka mikasu ga gwamnan jahar Zamfara a ranar Lahadi a garin Gusau.

KU KARANTA: NNPC: Mele Kyari ya canji Maikanti Baru a kamfanin mai na kasa

Daraktan watsa labaru na fadar gwamnatin jahar, Yusuf Idris ne ya bayyana haka, inda yace tun da fari yan bindigan sun sace mutanen da suka sako ne a kauyukan karamar hukumar Shinkafi da kauyen karamar hukumar Maru.

Da yake karbar mutanen daga hannun kwamishinan Yansandan jahar a fadar gwamnati, Gwamba Matawalle ya bayyana gamsuwarsa da matakin sulhun, wanda yace ana samun nasara daidai gwargwado, kuma yana sa ran matakin zai kawo dawwamammen zaman lafiya a Zmafara.

“Gwamnan ya bayyana farin cikinsa da cewa a kwanaki uku da suka gabata bai samu labarin satar shanu, garkuwa da mutane ko na kashe kashe a ko ina a jahar Zamfara ba, ba kamar yadda ake samu a baya ba, sa’annan gwamnan ya bukaci Yansanda su dage wajen magance ayyukan yan bindiga da dukkanin miyagun laifuka a jahar.” Inji shi.

Shima kwamishinan Yansandan jahar, Usman Nagogo ya jaddada manufarsu ta tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma tabbatar da zaman lafiya a jahar Zamfara.

Daga karshe gwamnan ya umarci a mika mutanen goma sha daya zuwa asibitin fadar gwamnatin domin likitoci su duba lafiyarsu kafin a sadasu da iyalansu da yan uwansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel