Sarkin Hadejia ya yabawa Gwamna Badaru na ba Izala gudumuwar filin Jami'a
Mai martaba Sarkin Hadejiya, Adamu Abubakar-Maje, ya jinjinawa gwamnan jihar sa na Jigawa watau Mohammed Badaru, bayan ya bada fili har eka 50 domin a gina jami’ar na Musulunci.
Mai girma Mohammed Badaru ya ba kungiyar nan ta Jama’atul Izalatul Bid’a Waikamatul Sunnah, JIBWIS wannan makeken fili ne domin ta gina katafariyar jami’a ta Musulunci a cikin jiharsa.
Sarki Abubakar-Maje ya yabawa gwamnan ne a lokacin da shugaban kungiyar ta JIBWIS na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya kai masa ziyara a fadarsa da ke cikin Garin Hadejiya Ranar Asabar.
Kamar yadda mu ka samu labari daga hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, kungiyar addinin Musuluncin ta JIBWIS ta na da fili yanzu wanda ya kai eka 115 da za ta gina wannan jami’a.
KU KARANTA: Za a gina asibitoci a sababbin Masarautun Jihar Kano
A baya kungiyar ta samu mallakar eka 65, daga baya kuma gwamna Badaru ya bada kyautar wasu eka 50, Wannan zai bada dama a fara shirin daura ginin babban jami’ar a Garin na Hadejiya.
Sarkin Hadejiya ya ji dadin yadda a ka zabi a gina wannan jami’a ta Musulunci a kasarsa. Mai martaban ya yi addu’ar a yi wannan aiki a kammala cikin sa’a a lokacin da ya ke na sa jawabi.
Babban shugaban kungiyar Izala, Lau, ya bayyana cewa ba da dadewa ba za a soma aikin wannan jami’a da za ta bada karfi wajen koyar da addinin Musulunci inda ya nemi Sarki ya sa albarka.
Shugaban karamar hukumar Hadejiya ya yi jawabi a taron a madadin sauran shugabannin kananan hukumomin Kirikasamma, Birniwa, Guri, Mallammadori, Kaugama, Auyo da K/Hausa.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng