Mai Neman Takarar Shugaba Kasa a ADC Ya Jero Hanyoyi 5 na Dakile Matsalar Tsaro
- Mai neman takarar shugaban kasa na ADC, Mohammed Hayatu-Deen, ya bayyana sabuwar dabarar dakile matsalar tsaro
- Hayatu-Deen ya yi alkawarin ayyana kungiyoyin ‘yan bindiga da masu garkuwa a matsayin ‘yan ta’adda tare da hukunta su
- Ya ce zai hada kai da kasashen Chadi, Nijar, Kamaru da Benin wajen yaki da ta’addanci da karfafa musayar bayanan sirri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC, Mohammed Hayatu-Deen, ya yi magana kan tsarinsa a Najeriya.
Hayatu-Deen ya bayyana wasu sababbin tsare-tsaren tsaro da tattalin arziki da zai aiwatar idan aka zabe shi shugaban kasa.

Source: Facebook
Hayatu-Deen ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata 12 ga watan Mayun 2026.
Hayatu-Deen ya kawo mafita kan matsalar tsaro

Kara karanta wannan
Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP
Ya ce matsalar rashin tsaro a Najeriya tana da alaka kai tsaye da matsalar tattalin arziki, yana mai cewa talauci da rashin tsaro suna kara jawo wa juna matsala.
Dan takarar ya ce karuwar rashin tsaro ta shafi noma, kasuwanci da samar da ayyukan yi, lamarin da ke bai wa kungiyoyin masu aikata laifi damar kara karfi.
Hayatu-Deen ya ce daya daga cikin matakan farko da zai dauka idan ya hau mulki shi ne ayyana wasu kungiyoyin masu laifi a matsayin kungiyoyin ‘yan ta’adda karkashin dokar hana ta’addanci.
Ya kuma yi alkawarin gurfanar da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu hada kai da su a gaban kotunan ta’addanci domin hanzarta yanke hukunci.
Hayatu-Deen ya ce zai umurci EFCC da CBN su gano tare da kwace kadarorin masu daukar nauyin ‘yan ta’adda, masu karbar kudin fansa da masu safarar makamai.
Dan takarar shugaban kasar ya kuma yi alkawarin sake farfado da rundunar MNJTF tare da kara hadin gwiwar tsaro da kasashen Chadi, Nijar, Kamaru da Benin.

Source: Twitter
Hanyoyi 5 da Hayatu-Deen zai kawo gyara
Hayatu-Deen ya kuma ce zai gyara tsarin tattara bayanan sirri tsakanin rundunar soja, ‘yan sanda, DSS, shige da fice da sauran hukumomin tsaro.
Ya kara da cewa zai inganta aikin ‘yan sanda ta hanyar horaswa, amfani da fasaha ta zamani da samar da tsarin gaggawar kai dauki a fadin Najeriya.
Daga cikinsu sun hada da:
1. Ayyana wasu kungiyoyi a matsayin yan ta'adda
2. Hukunta yan ta'adda da masu garkuwa
3. Lalata hanyoyin samun kudi masu garkuwa
4. Kawo karshen hannun gwamnati a biyan kudin fansa
5. Farfado da rundunar hadin guiwa ta MNJTF
Atiku, Hayatu-Deen sun sayi fom din takarar ADC
Mun ba ku labarin cewa 'yan siyasa daga jam'iyyu daban-daban na cigaba da sayen fom domin nuna sha'awar shiga takara a babban zaben 2027 da ake magana a kan shi.
A jam'iyyar adawa ta ADC, Atiku Abubakar da Mohammed Hayatu-Deen da manyan 'yan siyasa sun saye fom din takarar shugaban kasa.
Yayin da ake cigaba da shirye-shiryen 2027, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewa a Agustan 2026 za a fara kamfen.
Asali: Legit.ng
