Kwamishinan Bauchi da Ake Zargin Ya Wawure N4.6bn Ya Samu Izinin zuwa Aikin Hajji

Kwamishinan Bauchi da Ake Zargin Ya Wawure N4.6bn Ya Samu Izinin zuwa Aikin Hajji

  • Babbar Kotun Tarayya ta ba kwamishinan Bauchi, Yakubu Adamu, damar tafiya ƙasar Saudiya don gudanar da aikin Hajji da kuma duba lafiyarsa
  • Mai shari'a Emeka Nwite ya ba da umarnin sakin fasfo ɗin kwamishinan na ɗan lokaci domin ya sami damar gudanar da wannan tafiya daga 9 ga Mayu
  • Alkalin ya bayyana cewa kiyaye lafiyar ɗan adam ya fi komai mahimmanci, domin rayayye ne kawai ake iya yi masa shari'a har a yanke masa hukunci

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Mai shari'a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya ba kwamishinan kuɗi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu, izinin tafiya ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin 2026 da kuma neman lafiyarsa.

Alkalin ya yanke wannan hukunci ne a ranar Juma’a bayan duba buƙatar kwamishinan na neman izinin tafiyar da ayyukan Hajji na jihar Bauchi da kuma kula da lafiyarsa, inda a can za a yi masa aiki.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi garambawul a majalisar zartarwa da kwamishinoni 2 suka ajiye aiki

Kotu ta amince Yakubu Adamu da ake zargin ya wawure biliyoyin kudi ya tafi aikin Hajji
Jami'an hukumar EFCC sun kawo Yakubu Adamu, kwamishinan kudin Bauchi a babbar kotun tarayya Abuja. Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

Kwamishinan Bauchi ya samu izinin zuwa Hajji

Mai shari'a Nwite ya ba da umarnin sakin fasfo ɗin kwamishinan na ɗan lokaci domin ya sami damar gudanar da wannan tafiya wadda aka tsara za ta gudana tsakanin 9 ga Mayu zuwa 28 ga Mayu, 2026, in ji rahoton The Guardian.

Yayin nuna muhimmancin buƙatar, Mai shari'ar Nwite ya bayyana cewa rashin lafiya babban dalili ne mai ƙarfi da zai sa a saki takardun tafiyar wanda ake ƙara.

Ya ƙara da cewa:

“Babu shakka cewa rashin lafiya na iya zama babban dalili na musamman don amincewa da buƙata irin wannan.”

Mai shari'a Nwite ya jaddada cewa damar samun ingantacciyar kulawar lafiya haƙƙi ne na tsarin mulki da kuma jin ƙai, ba tare da la'akari da zargin laifin da ake yi wa mutum ba.

Kare lafiyar wadanda ake kara

Alkalin ya bayyana cewa kowa yana da haƙƙin samun kulawa, ko ana yi masa shari'a ko kuma yana tsare.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta musanta kashe mutane bayan nada Murtala Garo, ta soki Amnesty

Mai shari'ar ya buga misali da hukunce-hukuncen kotunan ɗaukaka ƙara, inda ya bayyana cewa kiyaye rai dole ne ya kasance babban fifiko a cikin harkokin shari'a.

Ya ce:

“Rayayye ne kawai yake iya bauta wa Allah. Kuma a sani cewa, rayayye ne kawai za a iya yi masa shari’a, a yanke masa hukunci, sannan a hukunta shi saboda ya aikata laifi.”

Sakamakon waɗannan hujjoji, kotu ta amince da dukkan buƙatun da wanda ake ƙara ya nema, in ji rahoton Punch.

Babbar kotun tarayya ta ce dole ne a kare lafiyar wadanda ake kara.
Harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: Light Oriye Tamunotonye / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Shari'ar da EFCC ke yi da kwamishinan Bauchi

Alkalin ya ba da umarni cewa a mika fasfo ɗin da Adamu ya ajiye a wajen magatakardan kotu a matsayin ɓangare na sharaɗan belinsa, na ɗan lokaci.

Ya kuma umurci kwamishinan da ya mayar da fasfo ɗin nan take bayan ya dawo Najeriya daga tafiyar.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ke shari'ar Yakubu Adamu tare da kamfanin Ayab Agro Products and Freight Company Limited kan zargin karkatar da kuɗaɗe da suka kai naira biliyan 4.6.

Kara karanta wannan

Tofa: Kotu ta bada umarnin kwace wasu kadarorin tsohon ministan Najeriya, Sylva

Kotu ta bada belin Yakubu Adamu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, kwamishinan kudi na Bauchi, Yakubu Adamu, da mutum uku sun san matsayarsu kan bukatar neman belin da suka yi.

Alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja ya amince da bukatar da mutanen suka nema ta samun beli a karar da hukumar EFCC ta shigar kansu.

Mai shari'a Mohammed Umar ya gindaya musu sharudda yayin da ya amince da bayar da belin na su a ranar Laraba, 21 ga watan Janairun 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com