Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ziyarci Tinubu

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ziyarci Tinubu

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan a yammacin ranar Lahadi, 7 ga watan Yuli ya ziyarci babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Ku tuna cewa Tinubu da sauran jiga-jigan jam’iyyar na kasa sun hada kai wajen ba Lawan goyon baya don ganin ya zama shugaban majalisar dattawa na tara.

A halin da ake ciki, shugaban majalisar dattawa ya bayyana cewa dole majalisar zartarwa da majalisar dokokin tarayya su hada kai wajen fidda yan Najeriya daga talauci.

Yayin da yake jawabi ga sanatoci a lokacin dawowa majalisa a rananr Talata, 2 ga watan Yuli a Abuja, Lawan yace akwai tsabar talauci a kasar kuma sai majalissun tarayya sun hada gwiwa sannan za a iya magance lamarin.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyyar PDP na gab da rushewa idan har aka tursasa Chinda a matsayin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai – Matasan PDP

Yace yana ta ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kalubalen da kasar ke fuskanta kuma cewa zai cigaba da yin haka a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa.

A yanayi mai kama da haka, Lawan a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuli ya ba yan Najeriya tabbacin kawo sauyi a kanfanin man fetir da gas na Najeriya, inda yake cewa Majalisan Dattawa ba tare da bata lokaci ba zata amince da dokar PIB.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin babban shugaban ExxonMobil Group of Companies, Pul McGrath wadan ya jagoranci tawagar shuwagabannin kamfanin zuwa ofishinsa a ranar Alhamis.

Lawan ya tuna a baya cewa wakilan majalisar da suka gabata sunyi iya kokarinsu, amman basu kai ga amincewa da dokar PIB din ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel