Allah sarki: Tsohuwa yar shekara 70 da jikokinta 4 sun rasa rayukansu a gobara

Allah sarki: Tsohuwa yar shekara 70 da jikokinta 4 sun rasa rayukansu a gobara

-Wata tsohuwa yar shekara 70, mai suna Moyo Jide, da jikokinta hudu sun rasa rayukansu a gobara da safiyar yau Asabar 6 ga watan Yuli 2019

-An bayyana cewa tsohuwar na zaune da jikokinta tun bayan rasuwar mahaifinsu

-Yan sanda sun bayyana cewa har yanzu ba a gano sanadin gobarar ba

Wata tsohuwa yar shekara 70, mai suna Moyo Jide, da jikokinta hudu sun rasa rayukansu a gobara da safiyar yau Asabar 6 ga watan Yuli 2019 a kauyen Biagbini dake a karamar hukumar Ese Odo dake a jihar Ondo.

Tsohuwar yar shekara 70 na zaune ne tare da jikokinta tun bayan rasuwar mahaifin yaran.

Gobarar ta tashi ne da dugu dugun safiyar Asabar a lokacin suna bacci wanda haka yayi sanadiyyar mutuwar tsohuwar da jikokinta guda hudu Jennifer yar shekara 3, Gbana mai shekaru 7, Bidaddy mai shekaru 5 da wisdom mai shekaru 9.

Har yanzu dai ba a san sanadiyyar gobarar ba, amma makwabtan gidan sun bayyana cewa ihun mamatan ne ya tayar da su kuma ahalin gidan sun kone kurmus kafin a taimakesu.

Wata majiya ta bayyana cewa gobarar ta tashi ne sakamakon barin wuta da akayi a dakin girkin gidan wanda haka ya sanya gidan ya kone kurmus.

KARANTA WANNAN: Safiya Badamasi: Bahaushiya ta farko da ta fara samun matsayin SAN

Ya bayyana cewa “Duka mutanen unguwarnan gobarar ce ta tayar da su tsakar dare lokacin da gobarar ta ashi, amma babu wani abu da aka iya yi don a ceto su. Komi na gidan ya kone kurmus.”

Ya bayyana cewa an sanar ma rundunar yan sanda game da afkuwar lamarin kuma an kai gawawwakin mamatan asibiti.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda na jihar, Femi Joseph ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya bayyana cewa an fara binciken sanadin tashin gobarar.

Joseph ya bayyana cewa “Har yanzu bamu gano sanadin gobarar ba amma mun fara bincike akan lamarin.”

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel