Najeriya ta gano sababbin hanyoyi 22 da zasu kawo mata kudade fiye da man fetir

Najeriya ta gano sababbin hanyoyi 22 da zasu kawo mata kudade fiye da man fetir

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta lalubo sababbin hanyoyin samun makudan kudaden shiga guda 22 da zasu maye gurbin man fetir, inji shugaban hukumar habbaka fitar da kayan kasuwanci daga Najeriya, NEPC, Segun Awolowo.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Awolowo ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin da yake ganawa da manema labaru a fadar gwamnati bayan wata ganawa da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a.

KU KARAN: Hankula sun tashi a Ibadan saboda hana dalibai mata sanya Hijabi a makarantar sakandari

Sai dai bai bayyana wadannan sabbin hanyoyi ba, amma Awolowo yace ya bayyana ma shugaban kasa tsare tsaren da suke yin a aiwatar da tsarin samar da kudaden shiga ba tare da dogara da man fetir ba, da kuma ayyukan da kwamitinsu yake yin a karkatar da akalar tattalin arzikin Najeriya daga mai.

A kwanakin baya ne majalisar zartarwa a karkashin jagorancin shugaban kasa Buhari ta kafa wata kwamiti a karkashin shugabancin gwamnan jahar Jigawa domin ta biciko hanyoyin samar da kudaden tafiyar da tattalin arzikin Najeriya, baya ga man fetir.

Awolow yace: “Duk da cewa farashin man fetir ya tashi, kuma shine yake baiwa Najeriya kashi 90 na kudaden shigarta, amma kasar ba zata iya dogaro kacokan ga man fetir ba, don haka gwamnati ke bukatar samar da wasu hanyoyin samun kudaden shiga na daban.

“Mun gano hanyoyi 22 da zasu kawo mana kudade baya da man fetir, muna fatan nan da shekaru 10 – 15 zamu samu kudi dala biliyan 150 daga hanyoyin nan.” Inji shi.

Awolowo yace suna daga cikin tsare tsaren da suke bi har da tsarin babban bankin Najeriya wajen baiwa manoman kadanya, tumatir, atarugu da koko bashin mai saukin ruwa domin su kara yawan abubuwan da suke nomawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel