‘Yan Sanda sun cafke Yarinyar da a ke zargi ta kashe babban Yayan ta a Jihar Kano

‘Yan Sanda sun cafke Yarinyar da a ke zargi ta kashe babban Yayan ta a Jihar Kano

Mun samu labari cewa wata Budurwa mai shekaru 19 a Duniya ta shiga hannun ‘yan sandan Najeriya inda a ke zargin ta da laifin kashe Yayan ta. Wannan abu ya faru ne a cikin Garin Kano.

A na zargin wannan Yarinya mai suna Mariya Sulaiman da su ke zaune a Unguwar Badawa da ke cikin Nasarawan Jihar Kano da laifin kashe ‘Danuwanta na jini Sani Sulaiman mai shekara 30 da wuka.

Mai magana da yawun bankin ‘Yan Sandan jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi, ya tabbatar da cewa an ruga da wannan Matashi zuwa asibitin Muhammad Abdullahi Wase lokacin da abin ya faru.

Ko da a ka isa asibitin, sai a ka tabbatar da cewa Sani Sulaiman ya cika. Yanzu dai wannan ‘Yaruwa ta sa ta na daure a hannun jami’an tsaro domin a binciki cikakken abin da ya faru inji DSP Abdullahi.

KU KARANTA: Annoba ta hallaka wasu Bayin Allah a cikin Garin Kano

‘Yan Sanda sun cafke Yarinyar da a ke zargi ta kashe babban Yayan ta a Jihar Kano

Mariya Sulaiman da ake tuhuma da laifin kashe Yayan ta a Jihar Kano
Source: Facebook

Rundunar ‘yan sandan na jihar Kano sun bayyana cewa rikici ya kaure tsakanin wadannan ‘Yanuwan ne bayan da Sani Sulaiman ya nemi a dakatar da wake-waken da a ka kunna a wurin biki.

Wani Bawan Allah da ya nemi a sakaya sunansa ya fadawa ‘yan jarida cewa Iyayen wadannan yara; Sule Ustaz da Mai dakinsa sun sume a lokacin da su ka ji labarin wannan mugun abin da ya faru.

Wannan mutumi wanda ya san wannan Iyalin da musiba ta auka masu ya fadawa Manema labarai cewa an ruga da Alhaji Sule Ustaz zuwa wani asibiti bayan ya fadi raga-raga a sakamakon rasuwar.

Kwamishinan ‘yan Sandan Kano, Ahmed Iliyasu ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike, kuma a nemi kotu ta hukunta wanda a ka samu da laifi. Ana zargin Mariya ta dabawa Sani wuka ne a wuya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel