Rashin Tsaro: An yi garkuwa da mutane 9, rayuka 73 sun salwanta a makon jiya cikin Najeriya

Rashin Tsaro: An yi garkuwa da mutane 9, rayuka 73 sun salwanta a makon jiya cikin Najeriya

Kimanin rayukan mutane 73 ne suka salwanta yayin aukuwar rikita-rikita da kuma tarzoma a fadin Najeriya cikin makon jiya da ya gabata. Rayukan wadanda suka salwanta sun hadar har da na jami'an tsaro.

A ranar Lahadin da ta gabata, rahotanni kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito sun bayyana cewa, 'yan daban daji sun salwantar da rayukan mutane 11 cikin wasu kauyuka 9 na karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.

Kauyukan da mummunan harin ya auku sun hadar da Pauwa, Katoge, Danhayi, Gidan Guge, Kaurawa, Jan Bago, Kadanya, Gidan Kwaki da kuma Lamabar Kantoma.

Kungiyar gwamnonin Arewa da sanadin shugaban ta gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ta yi Allah wadai da harin da ya auku a kan al'ummar Agatu ta jihar Benuwai inda rayukan kimanin mutane 25 suka salwanta.

Kuskuren fitar harsashin daga bindiga wani jami'in hukumar 'yan sanda reshen jihar Imo, ta salwantar da rayuwar wani mutum guda yayin da kuma daga bisani wani harin masu tayar da zaune tsaye ya salwantar da rayuwar wasu jami'an 'yan sanda uku a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa.

'Yan bindiga dadi sun harbe wasu jami'an 'yan sanda biyu murus a ranar Litinin cikin birnin Fatakwal na jihar Ribas. An kuma yi garkuwa da shugaban kwalejin kimiyar lafiya a karamar hukumar Gboko ta jihar Benuwe, James Ihongo.

'Yan daban daji a ranar Laraba ta makon da ya shude, sun salwantar da rayukan mutane 27 cikin yankuna daban-daban na jihar Katsina. Jaridar The Punch ta tabbatar da salwantar rayukan mutane 16 a karamar hukumar DanMusa ta jihar.

KARANTA KUMA: Son zuciya da son kai ya sanya matatun man fetur na Najeriya suka lalace - Shehu Sani

A can kuma cikin birnin Benin na jihar Edo, wasu 'yan bindaga sun yi awon gaba da wasu ma'aikatan wani kamfanin gilasai da karafa 'yan asalin kasar Sin bayan harbe dogarin su da harsashin bindiga da ya kasance jami'in dan sanda.

Wata bataliyar sojin kasa ta afka kan tarkon bama-bamai a garin Chibok na jihar Borno, inda rayuwar wani soji guda ta salwanta da misalin karfe 7.30 na safiyar ranar Alhamis jim kadan bayan rabuwar ta da Dajin Sambisa.

Kazalika 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutane biyu a yankin Agala-Iga na karamar hukumar Olamaboro ta jihar Kogi a ranar Alhamis. Makamancin wannan tsautsayi ya ritsa da wani jagoran al'umma, Matthew Ahmed tare da 'yan uwar sa inda a halin yanzu ake neman Naira miliyan 10 kudin fansar su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel