Yan bindiga sun kashe mutane 8 a kauyukan Katsina

Yan bindiga sun kashe mutane 8 a kauyukan Katsina

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun kashe mutane da dama a kauyukan Dan Sabau, Pawwa da Makera da ke karamar hukumar Kankara na jihar Katsina a daren ranar Asabar.

Mazauna yankin sun bayyana adadin mutanen da aka kashe a matsayin takwas, sannan yan sanda sun bayyana cewa mutane shida ne suka mutu.

An kuma tattaro cewa an sace dabbobi da dama.

A makon da ya gabata ne yan bindiga suka kashe mutane 18 a jihar.

Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah, a jiya Lahadi yace bayan sun samu wani kira, an tura tawagar jami’an tsaro sannan sun yi musayar wuta da yan bindiga na tsawon awa daya da rabi.

“Mun harbi da dama daga ikinsu, an kashe da yawa daga ikinsu sannan jami’an yan sanda ma sun ji rauni. Da daddare ne sannan yan bindigan sun yi amfani da bakaken kaya inda suke ta ihun Allahu Akbar.

“Tawagar sintirinmu na nan a yanzu suna zagayar yankin domin gano gawawwaki da makamai,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Allah sarki: Tsohuwa yar shekara 70 da jikokinta 4 sun rasa rayukansu a gobara

A wani labarin kuma, mun ji cewa matakin yin sulhu tsakanin yan bindiga da matasa yan sa-kai da gwamnan jahar Zamfara Bello Matawalle ya dauki gabaran yin a cigaba da samun tagomashi yayin da wata kungiyar yan bindiga ta sako mutane goma sha daya da take rike dasu.

Rahoton kamfanin dillancin labaru ya bayyana daga cikin mutanen da yan bindigan suka sako har da kananan yara guda 3, maza 5 da kuma mata 3, wanda aka mikasu ga gwamnan jahar Zamfara a ranar Lahadi a garin Gusau.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel