Akalla mutane 19 sun hallaka, 7 sun jikkata yayinda motoci 4 sukaci kicibis a jihar Kano

Akalla mutane 19 sun hallaka, 7 sun jikkata yayinda motoci 4 sukaci kicibis a jihar Kano

Mutane 19 sun rasa rayukansu yayinda kimanin mutane 7 suka jikkata a mumunan hadarin motan da ya faru a garin Dinyar Madiga, kusa da karamar hukumar Takai a jihar Kano.

Wannan mumunan ibtila'in ya faru ne da yammacin Lahadi, 7 ga watan Yuli, 2019 inda motoci hudu suka ci karo da juna yayinda suke kokarin kaucewa ramuka da suka cka hanyar.

Kwamandan hukumar kiyaye hadura FRSC na yankin, Zubairu Mato, ya bayyanawa manema labarai a ranar Litinin cewa wannan hadari ya faru ne misalin karfe 6 na yamma.

Ya ce hadarin ya shafi motoci hudu mallakan gwamnatin jihar Kano; kirar motocin sune Sharon, Golf, da Honda Civic.

KU KARANTA: Da duminsa daga kotun zaben shugaban kasa: An gabatar da Buba Galadima matsayin mai bada shaida

A cewarsa: "Samun labarin hadarin ke da wuya, sai muka tura jami'anmu wajen domin ceton rayukan wadanda abin ya shafa."

"Wadanda suka rasa rayukansu sune maza 14, mata 3, kananan yara 2 sannan 7 sun jikkata"

Mato ya laburta cewa babban musabbabin wannan hadari gangancin direbobi wajen gudu da kuma rashin kyawun hanya ne.

Yace hadarin ya faru ne lokacin da direbobin ke kokarin kauwacewa ramuka inda motoci suka kwace. An kai mutanen da abin ya shafa asibitin Takai inda likitoci suka tabbatar da cewa 19 sun rigamu gidan gaskiya yayinda sauran 7 na jibya.

Ya yi kira ga direbobi su rika bin dokar tiku domin kiyaye hadura da asarar rayuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel