Yadda Gwamnonin da su ka sauka su ka bar jama’a da makukun bashi

Yadda Gwamnonin da su ka sauka su ka bar jama’a da makukun bashi

Jihohi 12 da a ka samu canjin gwamnati a Najeriya su na dauke da bashin fiye da Naira tiriliyan 2 kamar yadda wani binciken da jaridar Daily Trust na Ranar 8 ga Watan Yulin 2019 ta yi, ya nuna.

Jaridar ta samu bayanan ta ne daga ofishin bashi na kasa na DMO, da hukumar da ke tara alkaluma a Najeriya, NBS da kuma sauran kwamitocin da gwamnoni ke nadawa domin karbar mulki.

Jihohin da a ka bar wannan tarin bashi duk da irin kudin da su ke samu daga asusun FAAC na gwamnatin tarayya da bashin Paris Club su ne irin su Borno, Imo, Adamawa, Gombe, Oyo, dsr.

Sauran wadannan jihohi sun hada Yobe, Bauchi, Nasarawa, Ogun, Zamfara, Kwara da Legas. Face Yobe, Legas, Bauchi da Adamawa, wadannan gwamnoni duk sun yi shekaru 10 ne a kan mulki.

KU KARANTA: Kudi da abin Duniya sun sa Iyaye saida Yaran da su ka haifa

Idan a ka tara bashin da tsofaffin gwamnonin wadannan su ka bari, za a samu fiye da Naira Tiriliyan 2. A haka ba a maganar kudin da wasu kananan ‘yan kwangila na cikin gida su ke bi.

Tsofaffin gwamnoni hudu; Yari, Dankwambo, Bindow, Abubakar da Ajimobi sun bar wa jihohinsu bashin Biliyan 612 kamar yadda takardu su ka nuna wajen mikawa sabon gwamnati mulki.

A Zamfara an bar bashin Biliyan 250, a Gombe kuma an bar wa jihar bashin Biliyan 110. Haka zalika gwamna Bindow ya bar bashin Naira Biliyan 115. A Oyo akwai bashin kudi na Biliyan 150.

Shi ma gwamna Mohammed Abubakar na Bauchi ya tafi ya bar jihar da bashin sama da Naira Biliyan 130. Sababbin gwamnonin jihohin ne dai su ka rika bayyana wannan hali da su ke ciki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng