Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Rahoton da muke samu na nuna cewa ana cigaba da garkuwa da mutane da a hanyar Abuja zuwa Kaduna yayinda yan bindigan sukayi awon gaba da fasinjojin mota kirar Golf da safiyar Litinin, 8 ga watan Yuli, 2019.

Yan bindigan sun tare da babbar titin Abuja zuwa Kadunan ne a daidadi gonar Mikati da jami'an yan banga ke tsayawa.

Wani mai idon shaida mai suna Idris Sa'idu ya bayyana hakan ne a shafin ra'ayi da sada zumuntarsa na Faceboob cewa saura kiris abin ya rutsa da su amma Allah ya kiyaye.

Yace: "Kidnappers (masu garkuwa da mutane) sun tarbe hanya sun kwashi mutane yanzunnan a hanyar Kaduna,Mu dai Allah Ya tsare mu, mun yi parking. Mota golf an kwashesu Kaf da direbobin wasu manyan motoci daidai labin gaban gonar Mikati inda yan banga ke tsayawa. Allah ya kyauta Amin."

A baya mun kawo muku rahoton cewa Duk da ikirarin sifeto janar na hukumar yan sanda, har yanzu ba'a daina garkuwa da mutane a kan babban titin Kaduna zuwa Abuja ba.

A makonnin da suka gabata, hukumomin tsaro a Najeriya sun karfara sintiri a hanyar yayinda garkuwa da mutane ya zama ruwan dare.

Mazauna garin Katari da Rijana inda da suka shahara da barayi da masu garkuwa da mutane sun bayyana cewa cikin makonni uku da suka gabata an samu sauki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel