Atiku Ya Dura kan Tinubu da Ƴan Bindiga Suka Kashe Tsohon Ɗan Majalisar Jigawa

Atiku Ya Dura kan Tinubu da Ƴan Bindiga Suka Kashe Tsohon Ɗan Majalisar Jigawa

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nuna bacin ransa kan mutuwar Hon. Abba Anas Adamu a hannun masu garkuwa da mutane
  • An sace tsohon dan majalisar ne a babban titin Kaduna zuwa Abuja ranar 3 ga Mayu, 2026, inda ya rasu a ranar 12 ga Mayu duk da kokarin ceto shi
  • Atiku ya bayyana faruwar lamarin a matsayin shaida na gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayukan yan kasar da take mulka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya nuna alhini da bacin ransa game da rasuwar Hon. Abba Anas Adamu, tsohon dan majalisar wakilai daga jihar Jigawa.

Legit Hausa ta ruwaito cewa, masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da Abba Adau a babban titin Abuja zuwa Kaduna a ranar 3 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Tsohon 'dan Majalisar tarayya, Anas Adamu ya rasu a hannun 'yan bindiga

Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Tinubu bayan 'yan bindiga sun kashe tsohon dan majalisar Jigawa.
Hon. Abba Adamu, tsohon dan majalisar da ya mutu a hannun 'yan bindiga da Alhaji Atiku Abubakar. Hoto: @iamHSDickson, @atiku
Source: Twitter

Martanin Atiku kan mutuwar tsohon dan majalisa

Bayan kwanaki tara ana fafutukar ganin an ceto shi, tsohon dan majalisar ya cika a hannun miyagun a ranar 12 ga watan Mayu, 2026, kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna.

A cikin wata sanarwa da hadiminsa Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya bayyana cewa:

“Mutuwarsa wata mummunar tunatarwa ce kan yadda tsaro ya rushe a karkashin gwamnatin Tinubu. Wannan ba rashi ne kawai ba, a’a, shaida ce ta gazawar gwamnatin da ta kasa sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata na kare rayuka da dukiyoyi.”

Atiku ya bayyana cewa Najeriya tana fuskantar barazana ta ko ta ina yayin da gwamnatin Tinubu ta koma kamar wadda abin ya fi karfinta ko kuma wadda ba ta damu da halin da mutane ke ciki ba.

Atiku ya magantu kan matsalar tsaro

Ya yi tambaya cewa idan har za a sace tsohon dan majalisa a daya daga cikin muhimman hanyoyin kasar nan har ya mutu a hannun 'yan bindigar, "wane fata ya rage wa talaka dan Najeriya?"

Kara karanta wannan

Tinubu ya kafa tarihi, ya kirkiri sabon ofishi a fadar shugaban kasa kan tsaro

Ya kara da cewa rashin tsaro ya zama ruwan dare a halin yanzu inda ake sace mutane a gidajensu, gonakinsu, da kuma kan hanyoyinsu na tafiya, in ji rahoton Vanguard.

Atiku ya caccaki yadda gwamnati ke yawan fitar da sanarwar tabbatar da tsaro wadda ba ta da wata alaka da halin kunci da mutane ke ciki a zahiri.

Atiku ya ce gwamnatin Tinubu ta gaza kare rayukan 'yan Najeriya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Alhaji Atiku Abubakar. Hoto: @atiku
Source: Twitter

Atiku ya kalubalanci gwamnatin Tinubu

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya sake jaddada cewa hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama filin kisan gilla duk da makudan kudaden da aka ce ana kashewa a bangaren tsaro.

Ya kalubalanci gwamnati da ta fito fili ta bayyana dabarun tsaron da take da su, maimakon dogaro da farfaganda da rubuce-rubucen 'karya'.

Atiku ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin da kuma daukacin al'ummar jihar Jigawa da ma Najeriya baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com