Matashiya ta mutu bayan ta saka 'sniper' a kan ta domin kashe kwarkwata

Matashiya ta mutu bayan ta saka 'sniper' a kan ta domin kashe kwarkwata

Wata matashiya, Ayomikun Juliana, da ke bautar kasa (NYSC) a garin Osogbo, babban birnin jihar Osun, ta mutu bayan an yi zargin ta shafa maganin kashe kwari mai karfin gaske (Sniper) a kan ta domin ta kashe kwarkwatar da ta dame ta.

Matashiyar ta je shagon gyaran gashi, inda aka gano cewa akwai kwarkwata a cikin gashin kan ta. Bayan ta dawo gida, sai ta yanke shawarar yin amfani da 'sniper' domin ta kashe kwarkwatar.

Matashiyar ta shafa maganin kashe kwarin kafin ta kwanta tare da yin amfani da hula ta rufe kan ta. Amma da safe sai aka same ta a sankame, kamar ta suma. An garzaya da ita zuwa asibiti domin ceto ran ta amma daga bisani ta ce 'ga garinku nan'.

Ko a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuli, Legit.ng ta kawo muku labarin cewa wani magidanci mai shekaru 51 ya jefa iyalinsa cikin damuwa bayan ya kwankwadi wani maganin kashe kwari mai karfin gaske (sniper) saboda ya dawo daga aiki ya kama matarsa turmi da tabarya ta na lalata da tsohon saurayinta.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Na kashe mutane fiye da 50, na samu kudi kusan miliyan N700 - Mai garkuwa da mutane

Magidancin, dan asalin kasar Zimbabwe, ya kashe matar ta sa sannan ya gaggauta shan maganin kwari.

Rahotanni sun bayyana cewa magidancin mai suna Simbarashe Chidaushe, mazaunin garin Gokwe, ya yi amfani da gatari wajen kashe matar bayan ya kama ta dumu-dumu ta na cin amanarsa da wani mutumin, sannan ya yi kokarin kashe kansa ta hanyar shan maganin kwari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel