Wani mutum ya kashe budurwar sa bayan ya sha kwayar Tramadol

Wani mutum ya kashe budurwar sa bayan ya sha kwayar Tramadol

Wani mutum mai shekaru 33 a duniya mai sunan Mojupa, ya gurfana a gaban kuliya da aikata babban laifin na kisan gilla. Mojupa ya shiga hannu da laifin kashe budurwar sa tun a ranar Talata 2, ga watan Yulin da ta gabata.

Ana zargin Mojupa da laifin kashe budurwar sa a unguwar Amuwo inda a cewar sa ya aikata hakan ne bayan ya sha wata muguwar kwaya mai sunan Tramadol da jefa shi cikin maye tare da yi masa karo.

Mojupa bayan amsa laifin sa gaban hukumar zartar da hukunci ta jihar Legas, ya yi ikirarin cewa ya aikata hakan ne a bisa umurnin wani mutum da ya hau kujerar naki wajen bayyana sunan sa. Ya kuma yi burus a kan rashin sanin matsugunnin wanda ya umurce shi a kan wannan aika-aika.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, wata budurwa mai shekaru 19 a duniya, Mariya Sulaiman, ta kashe dan uwan ta a jihar Kano bayan ya hanu su gudanar da shagalin fati na bikin auren wata 'yar uwar su.

KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: An yi garkuwa da mutane 9, rayuka 73 sun salwanta a makon jiya cikin Najeriya

Kwamishinan hukumar ‘yan Sandan Kano, Ahmed Iliyasu, ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike, kuma kotu za ta hukunta wanda a ka samu da laifi. Ana zargin Mariya ta dabawa dan uwan ta, Sani wuka ne a wuya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel