Maniyyatan Jigawa Sun Gamu da Matsala a Saudiyya, Barayi Sun Masu Tas a Makkah

Maniyyatan Jigawa Sun Gamu da Matsala a Saudiyya, Barayi Sun Masu Tas a Makkah

  • Abin takaci ya afku a Makkah da ke kasar Saudiyya bayan fashi ga wasu da ke ghudanar da aikin hajjin shekarar 2026
  • Majiyoyi sun ce wasu maniyyatan Jigawa uku sun rasa kudade da kayayyaki masu muhimmanci a lokuta daban-daban a kasar
  • Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jigawa ta bukaci mahajjata su kara sanya ido kan kayayyakinsu tare da yin taka-tsantsan a wuraren cunkoso da sufuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makkah, Saudiyya - Wani dattijo Bafullatani a jihar Jigawa ya bayyana cewa an yi masa fashin makudan kudi a Makkah.

Dattijon mai suna Baba Katanga daga kauyen Katanga da ke karamar hukumar Kiyawa ya ce ya rasa dala 400 bayan hawa tasi daga Masallacin Harami zuwa otel dinsa.

An yi wa mahajjata daga Jigawa fashi
Maniyyata da ke shirin shiga jirgi domin aikin hajji a Saudiyya. Hoto: National Hajj Commission of Nigeria.
Source: Facebook

Yadda aka yashe maniyya a Saudiyya

Rahotanni daga Daily Trust sun nuna cewa wasu alhazan Jigawa uku da suka je aikin Hajjin sun rasa kudade da kayayyaki masu muhimmanci sakamakon satar da ake zargin wasu barayi sun aikata.

Kara karanta wannan

"Yara na 3 sun mutu," Magidanci ya sabawa bayanin sojoji kan kuskuren jefa bam a Neja

Baba Katanga ya ce direban tasi ya yi amfani da lokacin da yake duba katin Nusuk dinsa wajen sace kudin ba tare da ya lura ba.

Dattijon ya ce:

“Na yi mamaki lokacin da na sake dubawa na gano dala 400 dina sun bace. Na shiga rudani saboda wannan ne kudin da zan yi amfani da su tsawon zamana."

A wani lamari daban, wani mahajjaci Bafullatani daga karamar hukumar Jahun shi ma ya rasa dukkan dalolinsa bayan da ake zargin wani direban tasi ya sace masa su.

Haka kuma wata mahajjaciya da aka fi sani da Hajiya ta rasa jakarta mai dauke da wayoyi biyu da kuma kudaden da za ta yi amfani da su yayin aikin Hajji.

An ce lamarin ya faru ne a Miqat da ke Madina, inda alhazai ke yin alwala da sanya ihrami tare da niyyar Umrah kafin tafiya zuwa Makkah.

Majiyoyi sun bayyana cewa matar ta bar jakarta na kusan mintuna biyu kafin ta dawo ta gano ta bace.

Lamarin ya jawo tausayi daga sauran alhazan Jigawa, inda wasu daga cikinsu suka hada kudade domin tallafawa wadanda abin ya shafa kafin hukumomi su dauki mataki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta gano kuskure, ta yi gyara a sunan da ake kiran Shugaba Bola Tinubu

Da yake mayar da martani, babban daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jigawa, Alhaji Ahmad Umar Labbo, ya tabbatar wa da alhazan cewa hukumar za ta taimaka musu domin rage musu radadin halin da suka shiga.

Labbo ya ce hukumar ta sha gargadin alhazai tun kafin tashinsu daga Najeriya da su kasance masu lura tare da kare kudade da kayayyakinsu daga masu aikata laifuka a wuraren cunkoso.

Ya bukaci mahajjata su guji bai wa baki amanar kayayyakinsu ko kuma barinsu ba tare da kulawa ba musamman a wuraren ibada da tashoshin sufuri.

Maniyyaci daga Taraba ya rasu a Saudiyya

An ji cewa an shiga jimami bayan rasuwar daya daga cikin maniyyatan da suka fito daga jihar Taraba kafin su tashi zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Maniyyaciyar wadda ta fito daga jihar Taraba ta rasa ranta ne awanni kadan kafin jirginsu ya tashi daga birnin Yola zuwa kasar.

Saudiyya Tuni aka yi wa marigayiyar jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a birnin Yola bayan samun amincewar danginta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.