Allah Ya tona asirin matashin daya shahara wajen satar wayoyin salula a Masallatai

Allah Ya tona asirin matashin daya shahara wajen satar wayoyin salula a Masallatai

Dubun wani matashi daya shahara wajen satar wayoyin salulan jama’a a cikin Masallatai a jahar Legas ta cika, a ranar Litinin 8 ga watan Yuli ne aka gurfanar da wannan matashi mai suna Wasiu Sosun gaban kotun majistri dake Legas.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa an gurfanar da matashin ne akan tuhumarsa da laifin sata da kuma daukan abinda ba nasa ba a gaban kotun majistri dake unguwar Tinubu na jahar Legas.

KU KARANTA: Sojoji sun tafka ma kungiyar Boko Haram mummunan ta’asa a Borno

Dansanda ma shigar da kara, Inspekta Ben Ekundayo ya shaida ma kotun cewa Wasiu dan shekara 21 ya aikata wannan laifi ne a ranar 28 ga watan Yuni a masallacin Kuti dake tsibirin jahar Legas.

Dansandan yace a wannan rana, Wasiu ya shiga cikin Masallacin ne inda ya yi kasake kamar yana Sallah, amma ashe ba sallah yake yi ba, kwantan bauna yake yi yana shirin cutar bayin Allah masu ibada.

“Sai da ya gama kallon masallatan tsaf, sai kawai ya wawuri wayoyin wasu masallata guda biyu, da darajarsu ta kai N8,000, kuma ya fita masallacin da gudu, don kuwa hatta jama’an da suka bi shi da nufin kamashi basu daman kama shi ba.” Inji Dansandan.

Dansandan yace laifin da Wasiu ya aikata ya saba ma sashi na 287 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Legas na shekarar 2015, kuma sashin ya tanadar da hukuncin zaman shekara uku a gidan yari ga duk wanda aka kama da laifin.

Shima Wasiu na take ya amsa laifinsa ba tare da ya baiwa sharia wahalaba, don haka bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, sai Alkalin kotun, mai shari A.M Olumide-Fusika ya bada umarnin garkame Wasiu a gidan Yari har zuwa ranar 18 ga watan Yuli kafin ya yanke masa hukunci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: