Latest
Wani magidanci mai da daya, wanda ‘yan sanda suka kwatanta da dan fashin da ba zai taba tuba ba, ya shiga hannun runduna ta musamman ta ‘yan sandan jihar Legas, a kan zarginsa da ake da kwacen wayoyi daga hannun mutane.
Akalla mutum ne guda daya ne ya rasa ransa yayin da wasu gungun miyagu yan bindigan daji suka kai farmaki ga wata ayarin matafiya a jahar Taraba, inda suka tasa keyar mutane 10 da nufin garkuwa da su.
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari, JAMB ta tsayar da ranar 13 ga watan Janairu a matsayin ranar da za ta fara sayar da takardar sha’awar zana jarabawar na shekarar 2020 ga dalibai masu sha’awa.
Mun ji cewa an hurowa karamin Ministan ilmi wuta a APC kan zargin hada-kai da PDP a zaben Imo. PDP dai ta ce a shirya ta ke ta karbe sa a jihar.
A cigaba da takalar juna tsakanin kasar Amurka da kasar Iran, wata kungiyar Shia ta jefa wasu rokokin bamabamai guda biyu zuwa ga ofishin jakadancin kasar Amurka dake Baghdad a kasar Iraqi.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi kira ka shugaban kasa Muhammadu Buhari daya daina fita kasashen waje domin duba lafiyarsa kamar yadda ya yi kira ga yan Najeriya, domin ya kasance shugaba nagari abin koyi.
Wanda su ka yi takara da Buhari a 2011 a CPC ya ba shi shawara cewa ya tsaida mai kishi a 2023 ba Marasa gaskiya da kuma wadanda su ke da giyar mulki ba.
Gungun yan bindiga dake fashi a kan teku sun halaka zaratan dakarun rundunar Sojin ruwan Najeriya guda hudu daga cikin Sojoji shida da suka kai agajin gaggawa ga wani babban jirgin ruwa da yan bindigan suka tare.
Jam’iyya mai mulki a matakin gwamnatin tarayyar Najeriya, jam’iyyar APC ta Baba Buhari ta yi wancakali da yunkurin farfadowar jam’iyyar PDP gabanin zagayowar zaben shugaban kasa na shekarar 2023, inda tace PDP ta yi ma Najeriya as
Masu zafi
Samu kari