Yan Najeriya sun wuce da saninku: APC ta yi fatali da yunkurin farfadowar jam’iyyar PDP

Yan Najeriya sun wuce da saninku: APC ta yi fatali da yunkurin farfadowar jam’iyyar PDP

Jam’iyya mai mulki a matakin gwamnatin tarayyar Najeriya, jam’iyyar APC ta Baba Buhari ta yi wancakali da yunkurin farfadowar jam’iyyar PDP gabanin zagayowar zaben shugaban kasa na shekarar 2023, inda tace PDP ta yi ma Najeriya asarar shekaru 16 da ta yi mulki a baya.

Haka zalika jaridar Premium Times ta ruwaito APC ta yi dirar mikiya a kan tsohon dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar bisa wani sako daya aika ma jam’iyyarsa a shafin Twitter, inda ya nemi su manta da batun takara a yanzu, su fara farfado da jam’iyyar.

KU KARANTA: Komai ta fanjama: An umarci Yansandan Najeriya su zama cikin shiri bayan kisan Janar Soleimani

A cikin sanarwar da APC ta fitar a ranar Lahadi, 5 ga watan Disamba, ta bayyana ma PDP da Atiku cewa sun zama tsofaffin yayi a siyasar Najeriya, don haka yan Najeriya sun wuce da saninsu, musamman yadda PDP ta barar da damarta a shekaru 16 da suka wuce da cin hanci da rashawa.

“Atiku na kokarin samar ma kansa tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ko kuma a wasu jam’iyyu na daban. Atiku da PDP sun zama tsofaffin yayi, wanda a yanzu yan Najeriya sun wuce da saninsu.

“An wuce lokacin da ake rabar da kadarorin Najeirya ga abokai, lokacin da ake bayar da kwangila, a fitar da kudin kwangilar ba tare da an gudanar da shi ba, lokacin da ake yi ma doka karan tsaye, lokacin da ake yi ma tattalin arzikin Najeriya dodorido, lokacin da cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare

“Amma a yanzu yan Najeriya sun samu sabon canji wanda ya tabbatar da samar da manyan ayyukan cigaba musamman aikin layin dogo, tituna, noma, sufurin jirgin sama, tashoshin jiragen ruwa, ilimi, kiwon lafiya, karkatar da tattalin arziki, cire ma’aikatan bogi da kuma hana aringizon kasafin kudi.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng