Auren Buhari: Za mu dauki mataki a kan wanda ya hada bidiyon bogi - Kwankwasiyya

Auren Buhari: Za mu dauki mataki a kan wanda ya hada bidiyon bogi - Kwankwasiyya

Kungiyar siyasar nan ta Kwankwasiyya ta bayyana cewa za ta dauki mataki a kan Kabiru Muhammad, wanda aka ce ya kirkiro bidiyon auren shugaba Buhari.

A cewar wannan kungiya wanda ta yi kaurin-suna a Najeriya, za ta hukunta Kabir Muhammad kamar yadda doka ta tanada, idan har bincike ya nuna cewa ‘Danta ne.

Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda shi ne Mai magana da yawun bakin ‘Dan takarar gwamnan jihar Kano a tutar PDP watau Abba Yusuf, ya bayyana wannan.

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fadawa Daily Trust cewa Kwankwasiyya ta na binciken lamarin domin gano ko cewa wannan Bawan Allah ‘dan cikin gidan na ta ne.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta taya Mataimakiyar Shugabar UN Mohammed murna

Auren Buhari: Za mu dauki mataki a kan wanda ya hada bidiyon bogi - Kwankwasiyya

Kwankwasiyya za ta binciki Yaronta da ake zargi da kago 'auren' Buhari
Source: UGC

“Da zarar mun gama bincikenmu, za mu sanar da Duniya matsayarmu. Idan wannan Mutumi da ake magana, Yaronmu ne, babu shakka za mu hukunta shi bisa doka.”

Malam Dawakin Tofa ya kara da cewa: “Saboda aikin da ya yi, ya sabawa akidar tafiyar Kwankwasiyya karara; don haka ba za mu dauki wannan abu da wasa ba.”

A cewar Dawakin Tofa, idan kuma ta tabbata cewa babu abin da ya hada wannan Bawan Allah da Kwankwasiyya, za su fito su yi magana domin su fitar da jama’a daga duhu.

Hadimin wani Jagoran tafiyar wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya ce su na bincike domin samun bayani a kan wannan Matashi da DSS ta kama fa laifin kago labarin bogi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel