Malami Ya Yi Abin Kunya, Kotu Ta Kama Shi da Laifin Dirka wa 'Yan Mata Ciki a Kwara

Malami Ya Yi Abin Kunya, Kotu Ta Kama Shi da Laifin Dirka wa 'Yan Mata Ciki a Kwara

  • Kotu ta samu babban limamim coci, Fasto Ajiboye Olayinka da laifin dirka wa kananan yara mata da aka ba shi amana ciki a wurin ibada a Kwara
  • Bisa haka, mai shari'a Hammed Gegele ya yanke masa hukuncin kare ragowar rayuwarsa a gidan gyaran hali
  • A cewar kotun, matan da abin ya shafa sun fuskanci tsoratarwa da matsin lamba, ciki har da tilasta musu rantsuwa da Littafi Mai Tsarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara, Nigeria - Babbar Kotun Jihar Kwara da ke zama a Ilorin, ta yanke wa fitaccen limamin coci, Fasto Ajiboye Olayinka hukuncin daurin rai da rai.

Kotu ta yanke wannan hukunci kan babban malamin na cocin Mission House of Divine Land of Joy and Prayer Ministry, bayan kama shi da laifin lalata da 'yan mata uku da ba su kai shekara 18 ba.

Kara karanta wannan

'Za a fara harbe su': Matakin gwamnatin Plateau kan makiyaya masu lalata gona

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a zaman shari'a a kotu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Alkalin babbar kotun jihar Kwara, Hammed Gegele ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba, 13 ga watan Mayu, 2026.

Kotu ta kama fasto da lalata da yara

Alkalin ya ce ya samu malamin addinin da aikata laifuffuka da suka shafi saduwa da kananan yara a cikin coci, zubar da ciki ba bisa ka'ida ba, da kuma mallakar makami ba tare da izini ba.

Alkali Gegele ya bayyana cewa wanda aka yankewa hukuncin ya yi amfani da matsayinsa na shugaban addini wajen yaudarar kananan yaran da aka danka masa amana da kuma keta musu haddi.

Yayin da yake karanta hukuncin, alkali ya ce:

"Wanda aka yanke wa hukuncin ya mayar da wadanda abin ya shafa tamkar injinan jima'i, inda ya ci zarafinsu a zahiri da kuma a zuciya."

Yadda faston ya rika yaudarar mata

Kotun ta ji bayanan yadda malamin cocin ya sha yi wa wasu daga cikin yaran ciki, sannan ya tilasta musu zubar da cikin tare da yi musu barazanar kisa idan suka tona asiri.

Kara karanta wannan

Uwargida ta cinna wa kishiyarta da ƴaƴanta 2 wuta a Kano, bayanai sun fito

A cewar kotun, wadanda abin ya shafa sun fuskanci tsoratarwa da matsin lamba, ciki har da tilasta musu rantsuwa da Littafi Mai Tsarki cewa ba za su taba fadar abin da ke faruwa ba.

Yayin da yake bayyana wanda aka yanke wa hukuncin a matsayin "fasiƙi," Alkali Gegele ya ce ayyukansa ababen kyama ne da ba za a taba amincewa da su ba a cikin kowace irin al'umma ta gari.

Jihar Kwara.
Taswirar jihar Kwara da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hukuncin da kotu ta yanke masa

Kotun ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai a laifuffguka uku mabanbanta saboda ketawa yan mata haddi.

An kuma yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 14 saboda zubar da cikin yaran, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kotu za ta rataye fasto a Akwa Ibom

A wani rahoton, kun ji cewa kotun jihar Akwa Ibom ta samu wani malamin addinin Kirista da hannu dumu-dumi a kashe wani dalibin jami'a.

Bisa jaka kotun ta yanke wa fa cocin Living Faith Church Chapel, Emmanuel Umoh, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mai shari’a Gabriel Ette na Babbar Kotun jihar ne ya yanke masa hukuncin bayan samunsa da laifin kashe ɗalibi a Jami’ar Uyo, Gabriel Bassey.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262