Yadda Netanyahu Ya Batar da Sawu Ya Shiga Kasar UAE Lokacin Yaki da Iran

Yadda Netanyahu Ya Batar da Sawu Ya Shiga Kasar UAE Lokacin Yaki da Iran

  • Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya shiga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) lokacin yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Benjamin Netanyahu ya shigar kasar UAE ne domin wata ziyarar sirri inda ya tattauna da shugabanta Sheikh Mohammed bin Zayed
  • Ofishin Firaministan Isra'ila ya bayyana muhimmancin ziyarar da Netanyahu ya kai da sakamakon da ta samar a dangantakar kasashen guda biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tel-Aviv, Isra'ila - Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya kai ‘ziyarar sirri' zuwa ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) lokacin yaƙi da Iran.

Benjamin Netanyahu ya ziyarci ƙasar UAE ne lokacin da ake yaƙi da Iran, kamar yadda ofishinsa ya sanar.

Netanyahu ya kai ziyarar sirri zuwa UAE
Benjamin Netanyahu, Firaministan kasar Isra'ila Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ofishin Firaministan Isra'ila ne ya fitar da sanarwar ziyarar Netanyahu zuwa UAE a shafin X a ranar Laraba, 13 ga watan Mayun 2026.

Me ya kai Benjamin Netanyahu kasar UAE?

Kara karanta wannan

Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, IGP Disu ya tsoma baki kan zargin kisan Dadiyata

Sanarwar ba ta bayyana abubuwan da shugabannin kasashen biyu suka tattauna ba ysyin ziyarar da Netanyahu ya kai a UAE.

Sai dai, ta bayyana cewa ziyarar ta samar da muhimmim ci gaba kan dangantakar d. Ke tsakanin Isra'ila da UAE.

Sanarwar na cewa:

“A tsakiyar gudanar da farmakin ‘Roar of the Lion,’ Firaminista Benjamin Netanyahu ya kai wata ziyarar sirri ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa inda ya gana da shugaban ƙasar, Sheikh Mohammed bin Zayed."
“Wannan ziyara ta haifar da gagarumin ci gaba mai matuƙar muhimmanci a dangantakar da ke tsakanin Isra’ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa."

Isra'ila ta ba UAE na'urorin kariya

Tashar Aljazeera ta ce sanarwar daga ofishinsa na zuwa ne kwana ɗaya bayan Jakadan Amurka a Isra’ila, Mike Huckabee, ya bayyana cewa Isra’ila ta aika da na’urorin kariya daga hare-haren sama na Iron Dome da kuma jami’an da za su sarrafa su zuwa ƙasar UAE lokacin yaƙin.

Benjamin Netanyahu ya kai ziyara zuwa UAE
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: @netanyahu
Source: Twitter

Iran ta fi kai wa ƙasar UAE hari fiye da kowace ƙasa lokacin yaƙin da aka fara a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Bayan mika fom din Tinubu, APC ta fadi tsarin tsaida dan takarar shugaban kasa

Duk da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da ta fara aiki a watan jiya, UAE ta bayar da rahoton hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa da dama daga Iran tun lokacin.

Ƙasar UAE tana ɗaya daga cikin manyan ƙawayen Amurka a yankin, kuma tana cikin ƙasashen Larabawa da ke da dangantaka da Isra’ila bayan sanya hannu kan yarjejeniyar Abraham Accords lokacin mulkin farko na Trump a shekarar 2020.

Isra'ila ta hukunta wasu sojojinta

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Isra'ila ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu sojojinta da suka ci mutuncin mutum mutumin mamar Yesu Almasihu a Kudancin Lebanon.

Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana cewa ta yanke wa sojojin guda biyu hukuncin ɗauri a gidan kurkuku bayan ta kammala bincike kan zargin da ake yi masu.

Ta bayyana cewa an yanke hukuncin ne bayan an ɗauki ɗaya daga cikinsu hoto yana sanya tabar sigari a bakin mutum-mutumin mamar Yesu Almasihu a Kudancin Lebanon.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng