Za’a fara sayar da fom din jarabawar JAMB a ranar 13 ga watan Janairu

Za’a fara sayar da fom din jarabawar JAMB a ranar 13 ga watan Janairu

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari, JAMB ta tsayar da ranar 13 ga watan Janairu a matsayin ranar da za ta fara sayar da takardar sha’awar zana jarabawar na shekarar 2020 ga dalibai masu sha’awa.

Shugaban sashin watsa labaru na hukumar, Fabian Benjamin ne ya sanar da haka a ranar Lahadi, 5 ga watan Janairu yayin da yake ganawa da manema labaru a jahar Legas, kamar yadda kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito.

KU KARANTA: Martanin PDP ga Buhari: Kai ne jagoran masu zuwa kasar waje domin duba lafiyarsu

A cewar Benjamin, hukumar ta kammala shirye shirye da duk wasu tsare tsaren fara sayar da takardar JAMB na bana daga ranar Litinin, 13 ga watan Janairu zuwa ranar Litinin, 17 ga watan Feburairu, a duk fadin Najeriya.

“A shirye muke, mun kammala duk wasu tsare tsare domin tabbatar da aiki ma kyau ba tare da samun tsaiko ba. Mun tantance tare da amincewa da cibiyoyin rajista da zana jarabawa guda 650 a shekarar 2020, muna fatan ba zasu bamu kunya ba.

“Mun bayyana musu yadda muke so a gudanar da aikin, kuma mun dauki matakai da zasu shawo kan duk wasu kalubale da zamu iya fuskanta ko su taso a yayin jarabawar, da kafin nan kuma bayan nan. Muna kara jaddada cewa babu ja da baya game da wajibcin amfani da lambar shaidar zama da kan kasa,NIN, kafin a sayar ma dalibi takardar JAMB din bana.” Inji shi.

Don haka hukumar JAMB ta yi kira ga duk daliban dake sha’awar zana jarabawar JAMB na bana dasu tabbata sun garzaya cibiyoyin da ake rajistan NIMC domin samu lambar shaida zama dan kasa na NIN.

Daga karshe hukumar ta sanar da masu sha’awar sayen takardar DE cewa a ranar daya za’a fara sayarwa tare da JAMB, kuma a kulle a rana daya, ba za’a tsawaita kwanakin ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel