Gwamna Inuwa Ya Gargadi Pantami da Sauran Masu Neman Takara a Gombe
- Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ja kunnen masu neman takara yayin da ake shirin gudanar da zabubbukan fitar da gwani
- Muhammadu Inuwa Yahaya ya ja kunnen 'yan siyasa kan tayar da zaune yayin gudanar da zabubbukan na fitar da gwani
- Gwamnan da zai bar ofis a Mayun 2027 ya bayyana cewa duk wanda aka samu da yunkurin tayar da zaune tsaye zai fuskanci hukunci mai tsauri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu game da tada rikici gabanin gudanar da zaɓubbukan fitar da gwani na jam’iyyu don babban zaɓen 2027.
Gwamna Inuwa ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta raga wa duk wani mai karya doka ko tada tarzomar siyasa ba.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga al'ummar jihar a ranar Laraba, 13 ga watan Mayun 2026.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi jawabi
Gwamnan ya ce ana sa ran jam’iyyun siyasa a faɗin jihar za su gudanar da zaɓubbukan fitar da gwani ne daidai da tanadin dokar zaɓe ta 2026 da kuma ƙa’idojin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
“Kamar yadda ku ka sani, shirye-shiryen babban zaɓen 2027 sun kankama. Ana sa ran jam’iyyun siyasa za su gudanar da zaɓubbukan fitar da gwani na ’yan takara daidai da dokar zaɓe ta 2026."
- Gwamna Inuwa Yahaya
Inuwa ya yi maganar zaben fitar da gwanin APC
Gwamnan ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ta fara gwada matakin yin maslaha ne da goyon bayan manyan jam’iyyar da shugabanninta na jiha, inda ya bayyana tsarin a matsayin wanda ya yi nasara sosai.
“Masu neman takara da dama sun amince sun goyi bayan ’yan takarar da muka amince da su a muƙamai daban-daban. Sai dai, ba a samu cikakkiyar maslaha ba saboda saɓanin fahimta daga wasu kalilan daga cikin masu neman takarar."
- Gwamna Inuwa Yahaya
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa rashin samun amincewar bai-ɗaya kan tsarin maslahar ya sanya zaɓen fitar da gwani na kato bayan kato ya zama dole.

Source: Facebook
Wane gargadi Gwamna Inuwa ya yi?
Har ila yau, ya yi gargaɗin cewa an ba wa jami’an tsaro umarnin su ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki kan duk wanda ya yi ƙoƙarin dagula zaman lafiya yayin zaɓen fitar da gwani ko bayan kammalawa.
“Bari na fito fili na faɗa: ba za mu amince da tashin hankali, rashin bin doka, da rashin ɗa’ar siyasa daga kowane mutum ko ƙungiya ba."
“Duk wani mutum ko ƙungiya, ko ma mene ne matsayinsa, idan aka same shi da hannu a tada zaune-tsaye kafin, lokacin, ko bayan zaɓubbukan fitar da gwani, zai fuskanci hukunci mai tsanani na shari’a."
- Gwamna Inuwa Yahaya
Pantami ya gargadi APC a Gombe
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya gargaɗi jam’iyyar APC kan zaben fitar da gwani na gwamnan Gombe.

Kara karanta wannan
Pantami ya bayyana muhimmancin zaben fitar da gwani ga jam'iyyar APC, ya yi gargadi
Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa sahihancin zaɓen fitar da gwani na takarar gwamna a jihar Gombe ne zai nuna ƙarfin jam’iyyar na cikin gida.
Tsohon ministan ya ƙara da cewa dimokuraɗiyyar cikin gida da adalci suna da matuƙar mahimmanci ga dorewar dimokuraɗiyya a Najeriya.
Asali: Legit.ng

